Isra'ila Vs Falasɗin: Iran Ta Nemi Taimakon Ƙasashen Musulmi, Ta Nuna Takaici
- Ƙasar Iran ta bayyana takaicin yadda duniya ta zuba idanu kan yadda Isra'ila ke cigaba da cin zalin Falasɗinawa
- Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian ya yi kuwwar neman haɗin kan ƙasashen Musulmi kan matsalar
- Shugaba Pezeshkian ya ce dole sai Musulmi sun haɗa kai wajen kawo ƙarshen zaluncin Isra'ila a kasar Falasɗin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Tehran, Iran - Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian ya ce akwai bukatar kasashen Musulmi su fara daukar matakin kawo ƙarshen ta'addancin Isra'ila.
Shugaban Masoud Pezeshkian ya yi kiran ne a lokacin da ya karbi bakuncin Ministan harkokin ƙasashen waje na Qatar, Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al Thani.
Jaridar Xinhua net ta wallafa cewa shugaba Pezeshkian ya ce lokaci ya yi da dukan ƙasashen Musulmi da ke mutunta dokar ƙasa da ƙasa za su cure wuri guda.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce zaluncin da ake yiwa Falasɗinawa, musamman mazauna zirin Gaza ya wuce yadda hankali zai ɗauka.
Falasɗin: Iran ta yabi Qatar kan tsagaita wuta
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa kasar Iran ta yaba da ƙoƙarin gwamnatin Qatar wajen cimma tsagaita wuta a Gaza, Falasɗinu da ya ƙi ci, ya ƙi cinyewa.
Shugaban ƙasar, Masoud Pezeshkian ne ya yi yabon a lokacin da ya zargi ƙasashe masu iƙirarin kare haƙƙin ɗan Adam da yin biris da kisan kiyashin da ake a Falasɗinu.
Ana samun ƙaruwar zaman ɗar-ɗar a yankin Gabas ta Tsakiya bayan Isra'ila ta kashe shugaban Hamas, Isma'il Haniyeh da na Hezbollah, Fouad Shokor a watan Yuli.
Turai ta ƙaƙabawa Iran takunkumi
A wani labarin kun ji cewa Kungiyar Tarayyar Turai (EU) ya hora Iran ya hanyar sanya takunkumi bayan ta kai harin ramuwar gayya ƙasar Isra'ila.
EU ta ɗauki matakin ne bayan tashi daga taron gaggawa kan harin, inda ake sa ran zai shafi ƙere-ƙeren jirage mataƙi da makamai da ta kai harin da su.
Asali: Legit.ng