Yusuf Bichi Ya Yi Murabus: Tinubu Ya Nada Sabon Shugaban Hukumar DSS

Yusuf Bichi Ya Yi Murabus: Tinubu Ya Nada Sabon Shugaban Hukumar DSS

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin Adeola Oluwatosin Ajayi a matsayin sabon shugaban hukumar DSS
  • Nadin Adeola Ajayi na zuwa ne bayan murabus din Yusuf Magaji Bichi wanda ya ke rike da mukamin tun a shekarar 2018
  • Mai magana da yawun shugaban kasa ne ya fitar da sanarwar nadin inda ya ce Tinubu ya bukaci Ajayi ya inganta DSS

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya nada Adeola Oluwatosin Ajayi a matsayin sabon Darakta-Janar na hukumar tsaro ta farin kaya (DSS).

Cif Ajuri Ngelale, mai magana da yawun shugaban kasa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi artabu da miyagu, an sheke 'yan bindiga a Katsina

Yusuf Magaji Bichi ya yi murabus daga shugaban hukumar DSS, Tinubu ya nada sabo
Shugaba Tinubu ya nada sabon shugaban hukumar DSS bayan murabus din Yusuf Bichi. Hoto: Abba Yusuf Bichi
Asali: Facebook

DSS: Yusuf Bichi ya yi murabus

A sanarwar da Cif Ajuri ya fitar a shafinsa na Facebook ya bayyana cewa Ajayi ya maye gurbin Yusuf Magaji Bichi wanda tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada a 2018.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun bayyana cewa Yusuf Magaji Bichi, ya yi murabus a ranar Litinin, 26 ga watan Agusta, sannan ya mika takardar murabus dinsa ga shugaban kasa Bola Tinubu.

Wannan lamari dai ya fito ne daga bakin wasu daga cikin masu ruwa da tsaki a hukumar, inda suka tabbatar da cewa Bichi ya sanar da na kusa da shi matakin da ya dauka.

Kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito, majiyoyi sun bayyana cewa Tinubu zai sanar da sabon shugaban hukumar domin samun sauyi cikin sauki da kuma ci gaba da gudanar da ayyukanta.

An nada Ajayi shugaban hukumar DSS

Kara karanta wannan

Shugaban hukumar NIA ya hadu da Tinubu, ya gabatar masa da takardar ajiye aiki

Sabon Darakta-Janar na DSS, Mista Adeola Ajayi, ya taka matakai masu yawa kafin ya kai kai matsayin mataimakin darakta janar na hukumar.

Ya yi aiki a lokuta daban-daban a matsayin daraktan hukumar na jiha a Bauchi, Enugu, Bayelsa, Ribas, da Kogi.

Shugaba Tinubu na sa ran sabon shugaban hukumar DSS zai yi aiki tukuru domin inganta ayyyukan hukumar tsaron tare da samar da sakamako mai kyau.

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan hulda da jama'a, Fredrick Nwabufo ya wallafa sanarwar Ngelale a shafinsa na X.

Duba sanarwar a kasa:

Mahaifiyar Yusuf Bichi ta rasu

A wani labarin, mun ruwaito cewa Hajiya Kareematu Abubakar Bichi, mahaifiyar shugaban hukumar DSS, Yusuf Magaji Bichi ta kwanta dama.

Shugaba Muhammadu Buhari a wata sanarwar ta'aziyya da ya fitar, ya bayyana marigayiya Hajiya Kareematu wanda ta rasu tana da shekaru 96 a matsayin mutuniyar kirki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.