Mace mace a Kano: Mahaifiyar shugaban hukumar DSS ta rasu a Bichi
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajanta ma shugaban hukumar tsaro na sirri, DSS, Yusuf Magaji Bichi biyo bayan rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Kareematu Abubakar Bichi.
Buhari ya mika sakon ta’aziyyar tasa ne ta bakin babban hadiminsa na musamman a bangaren watsa labaru da kafafen sadarwar, Malam Garba Shehu a ranar Lahadi, 26 ga watan Afrilu.
KU KARANTA: Da dumi dumi: An sallami mutane 10 da suka warke daga cutar Coronavirus a Legas
A sakon jaje da taya alhinin, shugaban ya bayyana marigayiya Hajiya Kareematu wanda ta rasu tana da shekaru 96 a duniya a matsayin mutuniyar kirki wanda maye gurbin ta zai yi wuya.
“Na ji zafin rasuwar Hajiya Kareematu, muhimmiyar mace a cikin al’ummarta, wanda tarihi ba zai manta irin kokarin da ta yi ba wajen hada kan iyalan ta da tabbatar da zaman lafiya a alummarta ba.
“Ina fata Allah Ya jikan Hajiya Bichi, Ya mata rahama, kuma Ya baiwa iyalanta, yan uwa da abokan arzikin hakurin juriyar rashin ta, Amin” Inji shi.
Idan za’a tuna a makon da ta gabata ne dai aka dinga samun mace macen mutane a jahar Kano sakamakon wani dalili ko wata cuta da ba’a san tabbacinsa ba.
Sai dai jama’a sun danganta mace macen ga annobar Coronavirus, yayin da wasu kuma suke ganin cututtuka ne da aka saba dasu suke kashe mutane sakamakon rashin aiki a asibitoci.
Sai dai gwamnatin Kano ta bakin kwamishinan watsa labaru, Muhammad Garba ta bayyana dalilan da suka sabbaba mace macen da aka dinga samu a jahar Kano a makon da ta gabata.
A cewar gwamnatin jahar, mace macen na da alaka da cututtukan hawan jini, ciwon siga, sankarau da kuma cutar zazzabib cizon sauro da suka dade suna addabar jama’an jahar.
Garba yace sun gano haka ne bayan sun gudanar da cikakken bincike game da mace mace, don haka yace mace macen basu da alaka da Coronavirus, saboda haka kada jama’a su firgita.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng