'Yan Ta'adda Sun Farmaki Tawagar Wani Kwamishina a Oyo, An Ga Hotunan Barnar

'Yan Ta'adda Sun Farmaki Tawagar Wani Kwamishina a Oyo, An Ga Hotunan Barnar

  • Wasu ‘yan ta'adda sun kai wa kwamishinan muhallin jihar Oyo, Mogbanjubola Olawale hari a lokacin da ya ke aikin shara a Ibadan
  • Kwamishinan da tawagarsa sun isa Mobil a Ibadan, domin aiwatar da aikin tsaftar muhalli a lokacin da maharan suka farmake su
  • ‘Yan tawagar Olawale sun samu munanan raunuka inda aka garzaya da su asibiti domin kula da lafiyarsu, yayin da motocinsu suka lalace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Oyo - Rahotanni da muke samu yanzu na nuni da cewa wasu da ake kyautata zaton 'yan ta'adda ne sun farmaki ayarin motocin kwamishinan muhalli na jihar Oyo.

An ce 'yan bindigar sun farmaki kwamishinan, Mojeed Mogbanjubola a ranar Litinin yayin da ya ke gudanar da wani aiki a Mobil, titin Ring da ke Ibadan.

Kara karanta wannan

Zulum ya sake yin rashi: Kwamishinan jihar Borno ya rasu a cikin dakinsa

Kwamishinan muhalli na jihar Oyo ya tsallake harin 'yan ta'adda
'Yan ta'adda sun kai wa kwamishinan muhalli na Oyo hari. Hoto: @seyiamakinde
Asali: Facebook

'Yan ta'adda sun farmaki kwamishina

Jaridar Leadership ta tattaro cewa kwamishinan tare da jami’an ma’aikatar muhalli da albarkatun kasa, suna aikin share tarkace a lokacin da ‘yan bindigan suka far musu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An lalata motocin gwamnatin jihar yayin da wasu daga cikin tawagar kwamishinan kuma suka samu raunuka yayin harin.

Rahotanni sun bayyana cewa an kai jami’an da suka jikkata zuwa asibiti domin yi musu magani.

"Ba za mu lamunta ba" - Hadimin gwamna

Jaridar OyoAffairs ta ruwaito cewa wani kakakin gwamnatin jihar Oyo ya yi magana kan harin.

Kakakin ya ce:

"Wannan lamari ne mai ban takaici wanda ke nuna kalubalen da muke fuskanta wajen kokarin kiyaye tsari da tsabta a cikin muhallinmu.
"Wannan harin ba zai karya mana kwarin guiwa ba kuma za mu ci gaba da yin aiki tukuru domin samar da yanayi mai kyau ga dukkanin jama'armu."

Kara karanta wannan

Mafi karancin albashi: Gwamnatin Kano ta yi magana kan shirinta, akwai gyare gyare

Tuni dai aka kira ‘yan sanda domin su binciki lamarin tare da kame wadanda suka aikata laifin, inji rahoton.

Kalli hotunan barnar da 'yan bindigar suka yi a nan kasa:

Kwamishina a Borno ya rasu

A wani labarin da muka fitar safiyar Litinin, 26 ga Agusta, mun ruwaito cewa kwamishinan kudi na jihar Oyo, Ahmed Ali Ahmed ya rasu a daki.

An ruwaito cewa sai da aka balle kofar dakinsa ne aka iya tabbatar da mutuwarsa bayan da aka ga lokacin fitowarsa da safe ya wuce bai fito ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.