Rahoton UNICEF: Gwamna a Arewa Zai Binciki Badakalar Sayar da Abincin Jarirai
- Gwamnatin jihar Sokoto ta ce za ta gudanar da cikakken bincike kan zargin karkatar da abincin jarirai da wasu ma'aikata suka yi
- Hukumar UNICEF ce ta yi ikirarin cewa wasu ma'aikata sun sace tare da sayar da abincin jarirai da aka rabawa cibiyoyin kiwon lafiya
- Kwamishiniyar lafiya ta jihar, Asabe Balarabe ta bayyana cewa gwamnati ba ta da masaniya kan hakan har sai da UNICEF ta yi magana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Sokoto - Gwamnatin jihar Sokoto ta ce za ta binciki zargin da asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya yi.
UNICEF ya yi zargin cewa an sace tare da sayar da abincin jarirai mai gina jiki da aka baiwa jihar domin inganta lafiyar yara masu fama da tamowa.
"An sace abincin jarirai" - UNICEF
A ranar Laraba ne jaridar Premium Times ta ruwaito cewa UNICEF ya bankado badakalar karkatar da abincin jarirai da ta rabawa jihar Sokoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban UNICEF na Sokoto, Kebbi da Zamfara, Michael Juma ne ya bayyana hakan a wani taron masu tsare-tsare na bayan wata uku da suke gudanarwa a Sokoto.
Ya ce wasu ma'aikata ne suka hada baki da 'yan kasuwa suka karkatar tare da sayar da abincin jariran da aka rabawa cibiyoyin kiwon lafiya daban daban a fadin jihar.
Gwamnati ta dauki mataki
Kwamishiniyar lafiya ta Sokoto, Asabe Balarabe, ta shaida wa Daily Trust cewa gwamnatin jihar ba ta da masaniya kan lamarin har sai da UNICEF ta fito da shi.
Asabe Balarabe ta ce:
“Mun fito daga taro kenan kan wannan batu. Ba za mu taba kyale maganar haka ba, dole ne mu yi bincike kuma mu hukunta masu hannu."
Ta ba jama’a tabbacin cewa gwamnatin jihar ta jajirce wajen ganin ta magance matsalar rashin abinci mai gina jiki ga jarirai, kuma za ta dauki matakin da ya dace kan barayin.
An gano badakalar ruwa a Kano
A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano, PCACC ta sake bankado wata dakalar kimanin N660m ta kwangilar ruwa da aka bayar.
An ce hukumar ta fara bin diddigin kudin da aka ware domin samar da ruwa a jihar wanda ake zargin an karkatar da kudin ba tare da aiwatar da kwangilar ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng