Hajiya Badiyya Inuwa ta bude sabon asibiti kyauta ga masu cutar sikila a Kaduna

Hajiya Badiyya Inuwa ta bude sabon asibiti kyauta ga masu cutar sikila a Kaduna

- Hajiya Badiyya Inuwa ta haifi yara guda biyu masu cutar sikila

- Daya ya rasu a lokacin yana dan shekara 13 sanadiyyar wannan cuta ta sikila

- Wannan daliline ya sanya ta bude wannan asibiti a cikin jihar Kaduna domin taimakawa marasa hali

A wata hira da aka yi da ita Hajiya Badiyya ta bayyana cewa ta haifi yara guda biyu wanda daya daga cikinsu ya mutu a lokacin yana da shekara 13 a duniya, sanadiyyar cutar sikila. Wannan dalili ne ya sanya Hajiya Badiyya Inuwa gina wata cibiya a cikin jihar Kaduna wacce take taimakawa talakawa wadanda suke fama da ciwon sikila ta hanyar ba su magunguna da kuma bada shawarwari.

A yanzu haka dai an bayyana cewa wannan cibiya tana taimakawa kimanin talakawa mutum dubu hudu (4000).

Hajiya Badiyya ta ce: "Duk inda na shiga a cikin Kaduna mutane na kirana da 'Mama Sikila', kuma ko yau na rasu na san nayi abin da baza a taba mantawa dani ba, kuma nayi wannan abu ne saboda dana da ya rasu sanadiyyar wannan cuta."

Mutane dai na taruwa a wannan cibiya don karbar magani kyauta da kuma samun fadaarwa.

"Na taba zuwa asibiti naga wata mata ta shiga wani hali sanadiyyar rashin lafiyar sikila da danta yake fama dashi, kwana biyu da zuwanta sai ake fada mini yaron nata Allah yayi masa rasuwa, sai ni kuma na nemi shawarar dana akan yadda zamu taimakawa talakawa masu sikila.

KU KARANTA: Roko nake Allah yasa Dangote yaga bidiyona ya aure ni - Inji Symba wata budurwa mai yin fim din batsa

"Mun fara bude wannan cibiya da mutane saba'in, tun daga wannan lokaci na saka aka je aka yi magana a rediyo cewa ga kungiyar da za ta tallafawa talakawa da magani kyauta."

Cibiyar ta zama wurin ceto rayuwar dubunnan mutane.

Ana haifar jarirai 150,000 da cutar kowacce shekara a Najeriya, kimanin kashi 50% zuwa 80% na yaran da ake haifa da cutar sikila a Najeriya na mutuwa kafin su kai shekara biyar a duniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel