Zulum Ya Sake Yin Rashi: Kwamishinan jihar Borno Ya Rasu a cikin Dakinsa
- Gwamnatin jihar Borno karkashin jagorancin Babagana Zulum ta yi rashin wani babban jami'i wanda rahotanni suka ce ya rasu
- Rahotannin da ke yawo sun bayyana cewa an tsinci gawar kwamishinan kudi na Borno, Ahmed Ali Ahmed a cikin dakinsa
- Kwamishinan labarai da tsaro na Borno, Usman Tar wanda ya tabbar da mutuwar kwamishinan a wata sanarwa ya yi bayani
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Borno - Kwamishinan kudi na jihar Borno, Ahmed Ali Ahmed, ya rasu ranar Litinin a gidansa da ke hanyar Damboa a Maiduguri, babban birnin jihar.
Majiyoyin da ke da masaniya kan lamarin sun ce an balle kofar dakin kwamishinan ne bayan da aka ga lokacin da ya saba tashi daga barci ya wuce.
Kwamishinan kudin jihar Borno ya rasu
Jaridar Daily Trust da ta fitar da rahoton ta ce kwamishinan ya rasu ne a cikin dakinsa, kuma iyalansa sun fahimci hakan bayan jinkirin fitowarsa da safe kamar yadda ya saba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Oga ya koma ga mahaliccinsa, ya rasu ne da safiyar nan."
- A cewar majiyar.
Gwamna Babagana Zulum tun bayan rantsar da shi karo na biyu a watan Mayun 2023 ya rasa kwamishinoni biyu da kuma mai ba shi shawara na musamman.
Gwamnatin Borno ta yi magana
Kwamishinan yada labarai da tsaro na jihar Borno, Usman Tar, ya tabbatar da mutuwar Ahmed a wata sanarwa da Channels TV ta samu.
Usman Tar ya ce za a yi jana'izar marigayi Ahmed a gidansa da yammacin ranar Litinin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
An rantsar da Ahmed a ranar 10 ga Agusta, 2024, kafin lokacin shi ne manajan bankin Zenith na jihar a Maiduguri.
Hadimin Zulum ya rasu a Borno
Legit.ng ta ruwaito cewa a ranar Asabar, 4 ga watan Mayu, 2024, mashawarcin gwamna Zulum na musamman kan hulda da jama'a, Cif Kester Ogualili, ya rasu.
Ogualili ya rasu ne a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri bayan ya sha fama da rashin lafiya.
Marigayin wanda ya fito ne daga karamar hukumar Dunukofia da ke jihar Anambra, ya shafe mafi yawan rayuwarsa a Borno.
Asali: Legit.ng