Tsohon Minista, Pantami Ya Kawo Hanyar Magance Ta'addancin Miyagun 'Yan Bindiga
- Farfesa Ali Isa Ibrahim Pantami ya yi magana kan matsalar rashin tsaro da ta daɗe tana ci wa ƙasar nan tuwo a ƙwarya
- Tsohon ministan na sadarwa ya bayyana cewa idan za a yi amfani da bayanan NIN da rajistar layi za a iya gano masu ɓarna
- Farfesa Pantami ya yi bayanin irin ƙoƙarin da ya yi a kan sace Sarkin Gobir wanda ƴan bindiga suka hallaka a hannunsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon ministan sadarwa a gwamnatin Muhammadu Buhari, Isa Ali Ibrahim Pantami, ya yi magana kan rashin tsaron da ake fama da shi a ƙasar nan.
Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya bayyana cewa akwai hanyar da za a iya shawo kan matsalar a samu a tsaro a ƙasar nan.
Me Pantami ya ce kan rashin tsaro
A cikin wani bidiyo da @el_uthmaan ya sanya a shafinsa na X, Farfesa Pantami ya bayyana cewa akwai hanyar da za a iya gano masu aikata ɓarna a ƙasar nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Farfesa Pantami ya yi bayanin cewa idan har za a yi amfani da kundin bayanan rajistar layi da lambar NIN babu wata ɓarna da za a yi ta tsaro ba tare da an gano ta ba.
Ya ce tabbas idan za a yi aiki da hanyar za a gano duk ɓarnar da aka aikata ko ba san waye ya yi ba ko kuma a ina ya aikata ɓarnar.
"Na sha faɗin cewa idan dai har za a yi aiki da kundin bayanan NIN da rajistar layi, ina nan kan baka na cewa babu wata ɓarna da za a yi ta tsaro da ba a san waye ba, ko ba a san a ina yake ba idan ba a san shi wanene ba."
- Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami
Ƙoƙarin Pantami kan sace Sarkin Gobir
Tsohon ministan ya bayyana cewa lokacin da ya samu labarin sace Sarkin Gobir ya yi ƙoƙarin ankarar da mutanen da ya sani suna harkar tsaro hanyar da za a iya gano inda yake.
Ya bayyana cewa yana da yaƙinin cewa bayanin da ya yi musu zai sanya ko dai ba a gano waɗanda suka sace shi ba, za a gano inda aka ajiye marigayin a lokacin.
Sojoji sun ragargaji ƴan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar sojojin saman Najeriya ta bayyana cewa jiragenta sun kai farmaki kan maɓoyar ƴan ta'adda a jihohin Kaduna da Zamfara.
Rundunar sojojin ta bayyana cewa a yayin farmakin, dakarunta sun hallaka ƴan ta'adda masu tarin yawa bayan sun yi musu luguden wuta.
Asali: Legit.ng