An Rasa Rayuka Bayan 'Yan Shi'a Sun Yi Arangama da 'Yan Sanda a Abuja
- An samu hargitsi a tsakanin jami'an ƴan sanda da ƴan ƙungiyar IMN mabiya Shi'a a birnin tarayya Abuja
- A yayin hargitsin an hallaka jami'an ƴan sanda mutum biyu tare da wani ɗan kasuwa da ke neman na abincinsa a kasuwar Wuse
- Rundunar ƴan sanda ta zargi ƴan Shi'an da kashe jami'an tsaron yayin da ƙungiyar ta fito ta musanta aikata hakan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - An harbe wani ɗan kasuwa, yayin da aka kashe jami’an ƴan sanda biyu a wata arangama da aka yi tsakanin ƴan ƙungiyar IMN mabiya shi'a da ƴan sanda kasuwar Wuse, Abuja.
Ɗan kasuwar da aka kashe an harbe shi ne a kirjinsa lokacin da yake gudu bayan ƴan sanda sun biyo ƴan Shi'a a kusa da Chateau De La-Rey a yankin Wuse Zone 6.
Arangama tsakanin ƴan sanda da ƴan Shi'a
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an cinnawa motocin ƴan sanda guda uku wuta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani ganau ba jiyau da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa ƴan Shi'an sun riƙa jifar ƴan sandan da duwatsu.
"Sun jefi ƴan sandan da duwatsu sannan suka ƙwace bindigogi a hannunsu. Sun fi ƙarfin ƴan sandan wanda hakan ya sanya suka arce. Sun ƙona motoci guda uku na ƴan sandan."
- Wani shaida
Ya ƙara da cewa yayin da ƴan Shi'an suka nufi wajen yankin Berger, ƴan sanda sun harba barkonon tsoguwa domin tarwatsu da sauran mutanen da ke wajen.
Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?
Da take martani kan lamarin, kakakin rundunar ƴan sandan birnin tarayya Abuja, Josephine Adeh, ta zargi ƴan Shi'a da kashe jami'an ƴan sanda.
"Ƴan Shi'a sun farmaki jami'an ƴan sanda inda suka hallaka jami'ai biyu tare da ƙona motarsu. Idan ka je wajen za ka ga cewa ƴan Shi'a ne suka farmaki ƴan sanda tare da hallaka su ba gaira ba dalili."
Josephine Adeh
Ƴan Shi'a sun musanta zargin
Sai dai, shugaban likitocin ƙungiyar IMN na Abuja, Ishaq Adam, ya musanta zargin da ƴan sanda suka yi.
Ya bayyana cewa an san mambobinsu da yin tattakinsu cikin kwanciyar hankali da lumana fiye da shekara 40.
Ƴan sanda sun hana taron ƴan Shi'a
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta ce ta haramta duk wani nau'i na taruka ba bisa ka'ida ba wanda kungiyar Shia'a ke gudanarwa ciki har da da tattakin ranar Ashura.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan, ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi a Kaduna.
Asali: Legit.ng