Jami'an Tsaro Sun Cafke Rikakkun Na Hannun Daman Bello Turji a Wani Bidiyo

Jami'an Tsaro Sun Cafke Rikakkun Na Hannun Daman Bello Turji a Wani Bidiyo

  • Ana cikin jimamin mutuwar Sarkin Gobir a Sokoto, wasu kasurguman yan bindiga sun shiga hannun jami'an tsaro
  • Jami'an tsaron sun yi nasarar cafke wasu daga cikin hatsabiban yan bindiga da ke karkashin dan ta'adda, Bello Turji
  • A cikin wni faifan bidiyo da aka yada, an gano yadda jami'an tsaro suka daure miyagun da dama bayan nasarar cafke su

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Sokoto - Jami'an tsaro sun yi nasarar kama wasu rikakkun yan bindiga a jihar Sokoto.

Daga cikin wadanda aka kaman sun hada da na hannun daman kasurgumin dan ta'adda, Bello Turji.

Yaran Bello Turji da dama sun shiga hannun jami'an tsaro a Sokoto
Jami'an Tsaro sun yi nasarar cafke na hannun daman Bello Turji a Sokoto. Hoto: HQ Nigerian Army.
Asali: Facebook

Sokoto: An cafke manyan yaran Bello Turji

Shafin Zagazola Makama shi ya wallafa faifan bidiyon yan ta'addan da aka kama a shafinsa na X a jiya Asabar 24 ga watan Agustan 2024.

Kara karanta wannan

Tallafin Tinubu: Basarake ya tabbatar da cafke shugaban APC kan almundahana

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zagazola Makama ya ce an cafke kasurguman yan ta'addan ne a iyakar Najeriya da Nijar da ke jihar Sokoto.

Jami'an tsaron sun yi nasarar cafke miyagun ne a wani samame da suka gudanar a kokarin dakile yan bindiga a yankin.

Su waye aka kama a jihar Sokoto?

Wadanda aka kaman ana zargin suna daga cikin yan ta'addan da ke aiki da Bello Turji da suka addabi jama'a da kashe-kashe a Arewa maso Yamma.

Samamen na daga cikin kokarin jami'an tsaro domin kakkabe dukan yan bindiga da suke kuntatawa al'umma a yankunan.

Wannan nasara na zuwa ne bayan mutuwar Sarkin Gobir, marigayi Alhaji Isa Bawa a jihar Sokoto a makon da ya gabata.

Bello Turji ya zargi Matawalle da ta'addanci

A baya kun ji cewa kasurgumin dan bindiga, Bello Turji ya zargi karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle da daukar nauyin ta'addanci.

Kara karanta wannan

Sarkin Gobir: Dattawan Arewa sun yi martani kan lamarin, sun tura sako ga Sultan

Dan ta'addan Turji musamman ya kira suna tsohon gwamnan Zamfara da cewa shi ya daurewa ta'addanci gindi wanda ya ki karewa.

Turji ya ce yana da hujjoji da zai kare zargin da ya yi na cewa gwamnatin da ta shude ita ta daurewa ta'addanci gindi a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.