Shugaban Hukumar NIA Ya Hadu da Tinubu Ya Gabatar Masa da Takardar Ajiye Aiki
- A yammacin yau Asabar, Ahmed Rufai Abubakar ya hakura da kujerar da yake kai na tsawon shekaru kusan bakwai
- Shugaban na hukumar NIA ya bukaci ya yi murabus kuma Mai girma shugaba Bola Tinubu ya amince da hakan
- Da ya je ganawa da shugaban kasa sai Ahmed Rufai Abubakar ya sauka daga matsayin da aka nada shi a 2018
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Darekta Janar na hukumar NIA, Ahmed Rufai Abubakar, ya gabatar da takardar barin mukamin da yake kai.
Ahmed Rufai Abubakar wanda Muhammadu Buhari ya nada a shekarar 2018 ya yi murabus daga shugabancin NIA a yau.
Ahmad Rufai Abubakar ya ajiye aiki
Daily Trust ta rahoto cewa Alhaji Ahmed Rufai Abubakar ya yi jawabi jim kadan bayan ya hadu da Bola Ahmed Tinubu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Darekta Janar na hukumar leken asirin ya godewa Bola Tinubu da ya ba shi damar yi wa kasarsa hidima bayan korar Ayo Oke.
Shugaban NIA ya je wajen Bola Tinubu
Ahmed Rufai ya ce ziyara ya kawo kamar yadda aka saba, lokaci bayan lokaci su kan yi zama da Mai girma shugaban Najeriya.
"Bayan zaman yau, na gabatar da takardar murabus dina kuma Mai girma shugaban kasa ya yarda, ya amince da ajiye aikin."
"Nagode masa da ya ba ni damar bautawa Najeriya a karkashin jagorancinsa na kawo sauyi, na Karin watanni 15, wanda abu ne da ba a saba gani ba, samun damar yin aiki da shugaban kasa biyu a jere."
"Saboda haka nagode masa sosai kuma na yi alkawarin zan cigaba da nuna kwarewa wajen bautawa kasarmu da hidimarta."
- Ahmad Rufai Abubakar
Meyasa Ahmad Rufai Abubakar ya bar NIA?
Tashar Channels ta ce Rufai bai fadi abin da ya sa ya sauka daga kujerar ba, ya ce akwai wasu jami’an da za su iya maye gurbin.
Jami’in tsaron yake cewa a kan samu dalili na gashin kai, iyali da sauransu, yake cewa alakarsa da Tinubu ba za ta yanke ba.
Kayode Ariwola ya bar kujerarsa
Rahoto ya zo cewa bayan biyu a matsayin alkalin alkalai kuma shugaban majalisar shari’a, Kayode Ariwola ya bar ofis a Najeriya.
A lokacin da yake ofis, an zargi babban alkalin da nada ‘ya ‘yansa da surukansa a matsayin alkalai da kuma alaka da 'Yan G5.
Asali: Legit.ng