Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya nada Mataimakan Shugaban NIA

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya nada Mataimakan Shugaban NIA

- An yi wasu nade-nade masu muhimmancin a Hukumar NIA

- Shugaba Buhari ya nada sababbin Mataimakan Shugabanni

- Daga cikin wadanda aka nada akwai wani Demenongu Agev

Dazu mu ke ji cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi wasu nade-nade na Mataimakin Darektoci a Hukumar leken asiri na kasa watau NIA. Kwanaki dai an ta jin surutu game da abubuwan da ke aukuwa a Hukumar.

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya nada Mataimakan Shugaban NIA
Buhari ya nada wanda za su taimakawa Shugaban NIA

Wadanda Shugaban kasar ya nada a matsayin Mataimakan Darektan su ne Demenongu Agev da Kio Solomon Benibo Ameiyeoferi. Abin da mu ka ji dai kurum shi ne Mista Agev ya fito ne daga Jihar Benuwe da ke Arewa ta tsakiya.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya gana da Gwamnonin Jam'iyyar sa

Shi kuma Solomon Benibo asalin sa mutumin Jihar Ribas ne da ke Kudu maso kudancin kasar. Wani Sakataren din-din-din a ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya Olusegun Adekunle ya sanar da wannan yace kuma tuni su fara aiki.

Wadannan Mataimakan dai za su rika agazawa Shugaban Hukumar tsaron na NIA wajen gudanar da ayyukan Hukumar. Idan ba ku manta ba a baya Legit.ng ta rahoto maku cewa an nada Ahmed Abubakar a matsayin Shugaban NIA.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng