Shin wanene tsohon Shugaban Hukumar tsaron kasa na NIA?
- Jiya Shugaban kasa Buhari ya kori Shugaban NIA
- Za ku ji ko ma shin dai wanene Ambasada Ayo Oke
- Ba mamaki yanzu Hukumar EFCC tayi ram da shi
Jiya ne mu ka ji daga Fadar Shugaban kasa cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya fatatattaki Shugaban Hukumar NIA Ambasada Ayo Oke daga aiki inda ya shirya yi wa Hukumar gyara na musamman. Jaridar Daily Trust ta kawo takaitaccen bayani game da Ayo Oke.
1. A Ranar 30 ga watan Oktoba Shugaban kasa Buhari ya sallami Ayo Oke daga aiki
2. Tsohon Shugaban kasa Jonathan ya nada Oke a Ranar 7 ga Watan Nuwamban 2013
3. Ambasada Ayo Oke ya maye gurbin da Ezekiel Olaniyi Oladeji ya bari ne a lokacin
4. Ayo Oke Bayarabe ne da ya fito daga Jihar Oyo daga bangaren Kudancin Najeriya
5. Oke yana rike da matsayin Darekta ne a Hukumar tsaron kafin ya dare Shugabanci
6. Ambasada Oke ya karanta ilmin tattali ne da siyasa a wata Jami’ar Kasar Amurka
7. Oke yayi aiki da Kungiyar Commonwealth ta Duniya a matsayin Jakada a baya
8. An sallame sa ne bayan an samu makudan Miliyoyin daloli na NIA boye a wani gida
Mai magana da bakin Shugaban kasa Garba Shehu ya bayyana cewa dai Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba Hukumar EFCC da ICPC dama tayi ram da Ayo Oke da Babachir David Lawal.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng