Farashin Dala a Lokacin IBB, Jonathan, Buhari, Tinubu tun daga 1979 zuwa 2024

Farashin Dala a Lokacin IBB, Jonathan, Buhari, Tinubu tun daga 1979 zuwa 2024

Abuja - A yanzu Naira ta yi wani mummunar faduwar da an yi shekaru ba a ga kamarsa ba a sakamakon matakan da CBN ya dauka.

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abin da rahoton nan ya yi shi ne tattaro farashin dalar Amurka daga lokacin da Shehu Shagari ya zama shugaban kasa zuwa yanzu.

An yi amfani da matsakaicin farashin kudin ketaren ne kuma ana la’akari ne da farashin babban banki ba na kasuwar bayan fage ba.

Dala.
Farashin Dala a lokacin mulkin shugabannin Najeriya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Statisense sun kawo wannan alkaluma ba tare da dogon bayani ba a shafinsu na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nawa Dala ta ke daga 1979-2024?

Kara karanta wannan

Dikko Radda da sauran Gwamnoni 6 da suka samu digirin PhD kafin shiga ofis

1. Shehu Shagari (N0.75K)

A lokacin da Shehu Usman Aliyu Shagari yake mulki, $1 ba ta kai N1 a Najeriya ba, kusan akasarin kimar Naira kenan har zuwa 1983.

2. Muhammadu Buhari (N0.9K)

A watanni 20 da Muhammadu Buhari ya yi a mulkin soja, Dala ta tashi daga N0.75 zuwa kusan N0.90K, duk da haka Naira ta fi daraja.

3. Ibrahim Babangida (N21)

Kafin Janar Ibrahim Babangida ya bar ofis a 1993, an rahoto cewa Dala ta tashi daga kasa da N1 a 1985, sai da ta zama fiye da N21.

4. Ernest Shonekan (N21)

Cif Ernest Shonekan bai dade yana rike da mulkin Najeriya ba, har zuwa lokacin da ya sauka, farashin dalar Amurka ba ta canza ba.

5. Sani Abacha (N21)

Nairametrics ta ce Haka lamarin yake a tsawon shekarun da Janar Sani Abacha ya yi mulki, zuwa lokacin da ya rasu, darajar $1 yana N21.

6. Abdussalami Abubakar (N94)

Bayan ganin karshen mulkin soja a 1998, Janar Abdussalami Abubakar yana kallo Naira ta rasa kimarta a kan kudin waje, Dala ta kai N94.88.

Kara karanta wannan

An yi korafin yadda Tinubu ya 'hana' Kashim Shettima rantsar da Shugabar Alkalai

7. Olusegun Obasanjo (N127)

A karkashin gwamnonin bankin CBN biyu, Naira ta tashi dafa N94.88 zuwa N127.89 da ya mika mulki ga Marigayi Ummaru Yar’adua.

8. Ummaru Yar’adua (N150)

Shugaba Ummaru Yar’adua ya rasu ya bar Dala ta na N150 a Najeriya. Daga hawansa mulki ya nada Mal. Sanusi Lamido ya rike CBN.

9. Goodluck Jonathan

Kudin Najeriya ya rasa kusan N50 na kimarsa a karkashin jagorancin Goodluck Jonathan, lokacin da zai mika mulki a 2015, Dala ta kai N197.

10. Muhammadu Buhari

A farashin babban banki, shugaba Muhammadu Buhari ya karbi Dala ne tana N197, a shekaru takwas da ya yi, sai da Dalar ta koma N461.6.

11. Bola Tinubu

Bola Tinubu bai dade a mulki ba, CBN ya karya Naira kuma ya daidaita kudin waje, wannan ya sa aka ji an saida Dalar Amurka har a N1, 600.

Shugabannin da suka koma neman PhD

Ku na da labari cewa tsofaffin shugabannin kasa kamar Olusegun Obasanjo da Yakubu Gowon sun samu PhD bayan barin mulki.

Shugabanni irinsu Atiku Abubakar sun iya sake shiga aji, suka samu shaidar digirin Masters a Ingila duk da cewa shekarunsa sun ja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng