Tsohon Sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi ya samu matsayi a jihar Kaduna

Tsohon Sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi ya samu matsayi a jihar Kaduna

- Gwamnatin jihar Kaduna ta nada Sanusi Lamido Sanusi mataimakin shugaban hukumar KADIPA

- Gwamna El-Rufa'i ne ya karbi bakwancin Sanusi Lamido Sanusi a bikin kaddamar da nadin

- Sanusi ya tabbatarwa gwamnatin jihar Kaduna goyon baya da aiki tukuru don kawo ci gaba a jihar

An nada tsohon Sarkin Kano kuma tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya, Sanusi Lamido Sanusi (Muhammadu Sausi II) a matsayin Mataimakin Shugaban Hukumar Raya Jarin Kasuwancin Kaduna, The Nation ta ruwaito.

Gwamna Nasir El-Rufai yayin da yake maraba da Sanusi a bikin kaddamar da hukumar ta KADIPA ya umarci ‘yan jihar da su rubanya kokarinsu na sanya jihar Kaduna a sahun gaba a duk inda ake saka hannun jari a Najeriya, ta hanyar inganta matsayin saukaka harkokin kasuwanci.

Gwamnan ya bayyana cewa KADIPA ta kasance babbar motar kai wa ga nasara a harkar saka jari a jihar, tana taimakawa tun daga 2015 don samun sama da $2.1bn a zahiri da kuma sanya hannun jari.

KU KARANTA: Ci gaba: Masana a Najeriya sun kirkiri allurar rigakafin COVID-19, saura gwaji kan mutane

Tsohon Sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi ya samu matsayi a jihar Kaduna
Tsohon Sarkin Kano Sanusi Lamido Sanusi ya samu matsayi a jihar Kaduna Hoto: Premium Times
Asali: UGC

El Rufa'i ya kuma nuna cewa KADIPA za ta yi takara ba kawai tare da sauran jihohin Najeriya don zuba jari ba; har ma da dukkan kasuwannin da ke shigowa, ya kara da cewa hukumar ba za ta huta ba a kan burinta na kokarin jawo 'yan kasuwa zuwa jihar Kaduna.

Ku tuna cewa Bankin Duniya ya sanya jihar Kaduna a matsayin mafi kyawun yanki a matsayinta na Saukin gudanar da Kasuwanci na 2018 da kuma a 2020.

Hakazalika Hukumar Bunkasa Harkokin Zuba Jari ta sanya jihar a matsayin ta farko a cikin adadin masu saka jari kai tsaye daga kasashen waje da aka ja hankali a cikin watanni shida na farkon shekara.

Da take amsawa a madadin sauran mambobi, Mataimakiyar Gwamnan jihar Kaduna kuma Shugabar Hukumar, Dakta Hadiza Balarabe ta bai wa Gwamnan tabbacin aniyarsu ta inganta tarihin KADIPA, saboda la’akari da yawan mutane da ke cikin Hukumar.

A nasa jawabin, sanannen masanin tattalin arziki, Sanusi II, ya yi alkawarin bayar da gudummawa mafi kyau don daukaka KADIPA sannan kuma zai ba da himma don samar da bayanai a cikin manufofin Gwamnatin Jihar Kaduna baki daya.

KU KARANTA: Ci gaba: Masana a Najeriya sun kirkiri allurar rigakafin COVID-19, saura gwaji kan mutane

A wani labarin, Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya rantsar da babban dan marigayi Mai Tangale a matsayin kwamishina, Daily Trust ta ruwaito.

Christopher Abdu Maisheru, dan marigayi sarkin, an rantsar dashi tare da Idris Abdullahi Kwami da Abubakar Aminu Musa, bayan tantancewa da tabbatarwa da su da majalisar dokokin jihar Gombe tayi.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Online view pixel