Dikko Radda da sauran Gwamnoni 6 da Suka Samu Digirin PhD Kafin Shiga Ofis

Dikko Radda da sauran Gwamnoni 6 da Suka Samu Digirin PhD Kafin Shiga Ofis

Abuja - A halin yanzu an fara samun ‘yan siyasar Najeriya da suka shigar harkar boko da gaske har suka iya samun digirin PhD.

A rahoton nan Legit Hausa ta kawo gwamnonin jihohin da ke ofis masu digirin na PhD, ba wannan ne karon farko da aka ga haka ba.

Gwamnoni masu PhD
Gwamnonin jihohi masu PhD a Najeriya Hoto: @ProfZulum. @CCSoludo, @Dikko_Radda
Asali: Twitter

Vanguard ta kawo gwamnonin da su kure wannan mataki da ilmin zamani a duniya.

Su wanene Gwamnonin da suke da PhD?

1. Babagana Zulum (PhD a injiniyan gona)

Tun a 2019 Farfesa Babagana Zulum ya zama gwamnan jihar Borno, yana cikin daidaikun Farfesoshin da suka taba zama gwamna a tarihi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A 1994 ya gama digirin farko a jami’ar Maiduguri, ya wuce Ibadan domin digirgir a bangarensa na injiniyan gona a 1998 sai ya samu PhD a 2009.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta bankado adadin masu digirin bogi daga kasashen waje

2. Charles Soludo (PhD a tattalin arziki)

Wani Farfesan da yake rike da kujerar gwamna a yau shi ne Charles Chukwuma Soludo da ya zama gwamnan Anambra a inuwar APGA.

A jami’ar Nsukka ya yi digirin farko da na biyu da na uku a ilmin tattalin arziki, daga baya ya zama Farfesa har ya iya zama gwamnan CBN.

3. Hyacinth Alia (PhD a ilmin addini)

Gwamnan Benuwai watau Hyacinth Alia ya fara karatunsa ne da difloma a ilmin addini a 1987, daga ya samu digiri a jami’ar Jos a Filato.

Faston ya je jami’o’in Fordham da Duquesne a Amurka domin yin digirgir. A kasar ta Amurka ne dai ya zama Dakta tun a cikin shekarar 2005.

4. Nasir Idris (PhD a malanta)

Mai girma Gwamnan jihar Kebbi ya samu shaidar babbar difloma da digirin farko a Birnin Kebbi da Sokoto a shekarar 1994 da 2003.

Kara karanta wannan

Sanusi II, Obasanjo, Gowon da wasu shugabannin da suka koma aji neman PhD

Nasir Idris ya samu digirin MBA a jami’ar Usmanu Danfodio a 2009 inda daga baya kuma ya zama dakta a bangaren ilmin malanta.

5. Dauda Lawal (PhD a kasuwanci)

Bayanan da aka samu daga shafin gwamnatin Zamfara ya nuna Dauda Lawal yana da B. Sc da M. Sc a ilmin siyasa daga ABU Zariya.

Ban da digirin PhD daga jami’ar Danfodio, gwamnan ya yi kwas a Oxford, Havard, Landan da manyan jami’o’in da ake ji da su a waje.

6. Ahmad Aliyu (PhD)

Ahmad Aliyu ya soma yin difloma ne a jihar Sokoto, hakan ya shi damar samun shaidar DPAA, a 1997 ya samu HND a Talata Marafa.

Bayan PGDM da ya yi a 2004, gwamnan na Sokoto ya yi digirin MBA a jami’ar Usmanu Danfodiyo kafin ya yi PhD a jami’ar Nasarawa.

7. Dikko Radda (PhD a harkar gona)

Bayan karatunsa a Katsina da Kafachan, Dikko Radda ya tafi jami’ar ATBU domin samun digirin B.Tech a harkar tattalin arzikin noma.

Kara karanta wannan

Wasu abubuwa 4 da za a tuna Alkalin Alkalai, Kayode Ariwola da su a Kotun Koli

Gwamna Radda ya yi digirin MSc da PhD a ilmin wayar da kan manoma a ABU a 2005 da 2015 bayan digirgrin MIAD duk a jami’ar.

Gwamna ya koma neman PhD

Ana da labarin cewa gwamna Umo Eno ya koma UNIUYO domin karasa digirinsa na uku watau PhD duk da irin hidimar da ke gabansa.

Gwamnan yana daf da samun wannan babbar shaida ne ya tafi yakin neman zabe, a karshe kuma ya zama gwamnan jihar Akwa Ibom.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng