Dubu Ta Cika: Yadda Aka Cafke Mai Garkuwa da Mutane a Cikin Masallaci

Dubu Ta Cika: Yadda Aka Cafke Mai Garkuwa da Mutane a Cikin Masallaci

  • Dubun wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne a jihar Taraba ta cika bayan ya shiga masallaci domin gudanar da Sallah
  • Wanda ake zargin an yi caraf da shi ne yayin da ya je babban masallacin Takum na jihar domin gudanar da Sallar La'asar
  • Dakarun sojoji sun kuma cafke wanda ya kitsa kisan da aka yiwa Hakimin Chanchangi da ɗansa a jihar Taraba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Taraba - An samu nasarar kama wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne a lokacin da yake sallah a cikin wani masallaci a jihar Taraba.

An cafke wanda ake zargin ne yayin da yake Sallah cikin wani masallaci a garin Takum na jihar Taraba.

Kara karanta wannan

Bayan kamfanin China ya kwace kadarori a waje, an kai gwamnatin Tinubu kotu a gida

An cafke mai garkuwa da mutane a Taraba
Dubun mai garkuwa da mutane ta cika a Taraba Hoto: Legit.ng
Asali: Original

An cafke mai garkuwa da mutane a masallaci

Wani mazaunin garin mai suna Dauda Mai Dawa ya shaidawa jaridar Daily Trust cewa an kama shi ne a lokacin da yake yin Sallar La'asar a babban masallacin Takum a ranar Juma’a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce an kama wasu mutane 13 da ake zargi a ranar a kan hanyar Takum-Maraban Baissa.

Sojoji sun cafke masu laifi a Taraba

A halin da ake ciki kuma, dakarun sojoji na Operation Whirl Stroke tare da haɗin gwiwar wasu hukumomin tsaro sun cafke wanda ake zargin ya kitsa kashe Hakimin Chanchangi da ɗansa.

Sojojin sun kuma kama wasu mutane 15 da ake zargi da yin garkuwa da mutane tare da ƙwato makamai da alburusai.

Kamen ya biyo bayan wasu ayyuka da sojojin suka gudanar a faɗin kananan hukumomin jihar Taraba.

Karanta wasu labaran kan garkuwa da mutane

Kara karanta wannan

Salatul Gha'ib: Bayani dalla dalla a kan sallar janazar da ake yi babu gawa

Jama'a sun cafke mai garkuwa da mutane

A wani labarin kuma, kun ji cewa al'ummar birnin Jos na jihar Plateau sun yi halin maza sun cafke wanda ake zargi da garkuwa da mutane bayan ya kama yara biyu.

Rahotanni sun nuna cewa mutumin da ake zargi ya karbi kudin fansa amma duk da haka ya ki ya sake yaran da ya yi garkuwa da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng