Tsadar Rayuwa: Tinubu Ya Sake Kwantar da Hankalin 'Yan Najeriya, Ya Ba da Tabbaci

Tsadar Rayuwa: Tinubu Ya Sake Kwantar da Hankalin 'Yan Najeriya, Ya Ba da Tabbaci

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da cewa ƴan Najeriya na fuskantar ƙalubalen matsalar tattalin arziƙi
  • Shugaba Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa na sane da buƙatun ƴan Najeriya kuma a shirye take wajen share musu hawaye
  • Ya bayyana aiwatar da tsarin sabon mafi ƙarancin albashi a matsayin ɗaya daga cikin matakan da ya ɗauka domin rage raɗaɗin da ake fama da shi a ƙasar nan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ce duk da ƙalubalen tattalin arziƙin da ƙasar na ke fuskanta, gwamnatinsa na sane da buƙatun ƴan Najeriya.

Kalaman nasa sun biyo bayan sukar da aka yi masa ne kan ƙin rage kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa, musamman kan siyo jirgin ruwa na alfarma da jirgin saman shugaban ƙasa da dai sauransu.

Kara karanta wannan

Kungiyar HURIWA ta bukaci Tinubu ya yi murabus, ta fadi dalili

Tinubu zai share hawayen 'yan Najeriys
Tinubu ya ce yana sane da bukatun 'yan Najeriya Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Gwamnatin Tinubu ta samu nasarori

Da yake jawabi a wajen bikin yaye ɗalibai karo na 32 na kwalejin tsaro ta ƙasa da ke Abuja, Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ta samu nasarori sosai wajen magance wasu ƙalubalen da ƴan Najeriya ke fuskanta, cewar rahoton The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Kashim Shettima, ya bayyana mafi ƙarancin albashin ma’aikata na N70,000 a matsayin ɗaya daga cikin matakan da aka dauka na magance matsalolin tattalin arziƙin da a ke fuskanta.

Tinubu ya yarda ana shan wuya

"Ƙasar mu tana fuskantar ƙalubale da yawa na zamantakewa da tattalin arziƙi. A matsayinmu na gwamnati, muna kula da buƙatun jama’armu. Za mu ci gaba da yin abubuwan da za su amfani mutanen mu."
"Kwanan nan, mun samu gagarumin ci gaba wajen magance wasu daga cikin waɗannan ƙalubalen."

Kara karanta wannan

Ceto daliban likitoci: 'Yan sanda sun bayyana kudin fansan da aka biya 'yan bindiga

"Mun aiwatar da tsarin sabon mafi ƙarancin albashi na ƙasa, wanda ba ma’aikata farar hula kaɗai za su amfana ba, har ma da jami’an sojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro."

- Bola Tinubu

Ya kuma ce gwamnatinsa na aiki tukuru domin daƙile satar ɗanyen man fetur domin tattalin arziƙin ƙasar nan ya zauna da ƙafarsa, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.

Ƴan Najeriya sun gaji

Muhammad Abba mazaunin jihar Katsina ya gayawa Legit Hausa cewa ƴan Najeriya sun gaji da gafasa sa ba su ga ƙaho ba.

Ya bayyana cewa gwamnati ta saba cewa tana sane da halin da ƴan Najeriya suke ciki amma babu wani abin da take yi domin tsamo su daga ciki.

"Kullum dai abu ɗaya ake ta faɗa cewa ana sane da halin da mutane suke ciki amma babu wani ƙoƙarin da ake yi domin a fitar da su daga ciki."

- Muhammad Abba

Kara karanta wannan

Ana jimamin kisan sarkin Gobir, 'yan bindiga sun sace matar basarake da 'ya'yansa 2

Gwamnatin Tinubu ta magantu kan rashin tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta bayyana cewa akwai buƙatar jami'an tsaro su mayar da hankali wajen kokarin sanya ido kan al'amuran tsaro.

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ne ya bayar da umarnin a taron kammala karatun kwalejin tsaro ta Nigeria Defence Academy da ke Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng