Kashim Shettima Ya Yi Takaicin Rashin Tsaro, Gwamnati Ta Daukarwa Najeriya Alkawari

Kashim Shettima Ya Yi Takaicin Rashin Tsaro, Gwamnati Ta Daukarwa Najeriya Alkawari

  • Gwamnatin tarayya ta umarci jami'an tsaro su kawo karshen matsalar tsaro da ke addabar sassan kasar nan
  • Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayar da umarnin a taron kammala karatun kwalejin tsaro a Abuja
  • Sanata Kashim Shettima ya ce kamata ya yi jami'an tsaro su tashi haikan kuma su zama masu sanya idanu kan lamuran tsaro

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa akwai bukatar jami'an tsaro su mayar da hankali wajen kokarin sanya ido kan al'amuran tsaro.

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ne ya bayar da umarnin a taron kammala karatun kwalejin tsaro ta Nigeria Defence Academy da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Majalisa ta gano inda tallafin buhunan shinkafar Tinubu ke maƙalewa

Kashim
Gwamnatin tarayya ta umarci jami'an tsaro su kawar da matsalar tsaro Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

Channels Television ta wallafa cewa Sanata Shettima, wanda ya wakilci shugaban kasa a taron ya ce gwamnatin tarayya na daukar matakan kawar da rashin tsaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce gwamnati na kokarin samar da yanayi mai kyau wanda zai jawo masu zuba hannun jari kasar domin bunkasa tattalin arziki.

Kashim Shettima nemi kawar da rashin tsaro

Vanguard News ta tattaro cewa gwamnati ta yaba da kokarin da jamuian tsaron kasar nan ke yi wajen tabbatar da kare dukiya da rayukan jama'a.

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da ya bayyana haka ya ce amma akwai bukatar samar da shugabanci mai tsarin da zai kawar da rashin tsaro.

Rashin tsaro: Gwamnati ta dauki alkawari

Gwamnatin Bola Tinubu ta dauki alkawarin tabbatar da kakkabe rashin tsaro daga fadin kasar nan.

Kashim Shettima ya ce gwamntinsu za ta cigaba da samar da tsare-tsaren da za su tabbatar da wanzuwar zaman lafiya da yalwar arziki tsakanin yan kasa.

Kara karanta wannan

Bayan kisan sarkin Gobir, gwamnatin Tinubu ta yi yunkurin kubutar da likitar da aka sace

Shettima ya fadi hanyar magance rashin tsaro

A wani labarin kun ji cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana hanyar da ya ke ganin za ta tabbatar da magance rashin tsaro.

Sanata Kashim Shettima ya bayyana cewa babbar hanya za ta taimakawa yakin da ake yi da ta'addanci ita ce tsaurara tsaro a iyakokin Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.