Alkali Ta yi Afuwa ga Fursunoni 44, Ta Gargadi Ɓarawon Tukunyar Mahaifiyarsa

Alkali Ta yi Afuwa ga Fursunoni 44, Ta Gargadi Ɓarawon Tukunyar Mahaifiyarsa

  • Babbar alkalin jihar Akwa Ibom, Mai shari'a Ekaete Obot ta yi afuwa ga fursunoni 44 a gidajen gyaran hali daban daban
  • Ekaete Obot ta bayyana cewa an duba wadanda suke da kananan laifuffuka ne da kuma suka dade ba tare da an shari'a ba
  • Alkaliyar ta yi jawabi na musamman kan wanda ya shafe sama da shekara a gidan yari saboda satar tukunyar uwarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Akwa Ibom - Babbar alkalin jihar Akwa Ibom, mai shari'a Ekaete Obot ta yi afuwa ga fursunoni 44 a gidajen gyaran hali.

Mai shari'a Ekaete Obot ta yi kira na musamman ga gwamnatin jihar Akwa Ibom kan inganta rayuwar fursunonin jihar.

Kara karanta wannan

An shiga jimami, tirela ta markaɗe tsohuwa da jikarta har lahira

Akwa Ibom
An yi afuwa ga yan fursuna a Akwa Ibom. Hoto: Legit
Asali: Original

Rahoton Channels Television ya nuna cewa alkalin ta yi bayani na musamman kan wani dan fursuna da ya sace tukunya a gidansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alkali ta yi wa fursunoni 44 afuwa

Mai shari'a Ekaete Obot ta tabbatar da yin afuwa ga yan fursuna 44 yayin da ta kai ziyara gidajen gyaran hali a jihar.

The Guardian ta wallafa cewa alkalin ta ce an zabi masu kananan laifuffuka ne da suka hada da satar kayan abinci, tukunya, yin fada tsakanin yan uwa.

An saki ɓarawon tukunya a Akwa Ibom

Wani mai shekaru 28 mai suna Shadrach Hanson ya shafe shekara daya da watanni hudu kan sace tukunyar mahaifiyarsa.

Alkalin ta ce an yi wa Shadrach Hanson afuwa kuma tana fata ya zama ɗa nagari ta inda ba zai sake dawowa gidan gyaran hali saboda aikata laifi ba.

Kara karanta wannan

Majalisa ta gano inda tallafin buhunan shinkafar Tinubu ke maƙalewa

Alkali ta yi kira ga gwamnatin Akwa Ibom

Mai shari'a Ekaete Obot ta yi kira na musamman ga gwamnatin jihar Akwa Ibom kan samar da makarantu a gidajen gyaran hali.

Ta kuma yi kira kan muhimmacin koyawa yan fursuna sana'o'i domin dogaro da kai idan suka fita daga gidan.

Babbar Alkali to koka kan yan siyasa

A wani rahoton, kun ji cewa babbar mai shari'a ta jihar Kano, Dije Abdu Abdullahi ta ce yadda bangarorin gwamnati ke yin katsalandan a bangaren shari'a na hana aiwatar da gaskiya.

Ta ce matukar ana samun masu shiga harkokin bangaren, ba za a samu adalci da gaskiyar da ake fatan samu daga lauyoyi da masu shari'a ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng