Bajau da su: Gwamna Bindow ya yiwa Fursunoni 33 afuwa

Bajau da su: Gwamna Bindow ya yiwa Fursunoni 33 afuwa

- Yau wasu 'yan Fursuna Murna bakinsu har kunne bisa sharbar romon Dimukuradiyya

- Gwamnan jihar Adamawa Muhammadu Bindow ya bayar da umarnin yin afuwa ga wasu Fursunoni 33 a wani bangare na cigaba da shagulgulan ranar Dimukuradiyya ta 29 ga watan Mayu.

Kwamishinan yada labarai da tsare-tsare na jihar Ahmad Sajoh ne ya bayyana haka a wata sanarwa da take dauke da sa hannunsa.

Bajau da su: Gwamna Bindow ya yiwa Fursunoni 33 afuwa
Gwamnan jihar Adamawa Muhammad Umar Jibrilla Bindow

Inda ya bayyana cewa Fursunonin da aka yiwa afuwar sun fito ne daga gidan kurkuku 5 na jihar.

Sanarwar dai ta bayyana cewa, “Mai girma Gwamnan jihar Adamawa Muhammad Umar Jibrilla Bindow ya amince da shawarar kwamitin jikai suka ba shi, tare kuma damar da yake da ita wadda kundin tsarin Mulki ya bashi a sashi na 212(I) (d) ya bayar da umarnin sakin Fursunonin 33 domin suma su sharbi roman Dimukuradiyya.”

KU KARANTA: Ranar Demokaradiyya: Batutuwa 5 da Shugaba Buhari ya tabo a jawabinsa

Fursunonin dai za’a sake su ne nan take ba tare da wani bata lokaci ba kasancewar an kammala duk wasu tsare-tsare ta fuskar shari’a.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa jadawalin Fursunonin da aka saka dai dukkanninsu Maza ne kuma 14 daga cikinsu sun fito ne daga Kurkukun Yola sannan 9 kuma daga Kurkukun Jada sai kuma 6 daga Kurkukun Mubi yayin da 3 kuma suka fito daga Kurkukun Numan da kuma wani 1 da aka dauko daga Kurkukun Jimeta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng