Ma'aikata za Su Caɓa, Gwamna Ya Fara Biyan Sama da Mutum 1000 Hakkokin Fansho

Ma'aikata za Su Caɓa, Gwamna Ya Fara Biyan Sama da Mutum 1000 Hakkokin Fansho

  • Gwamnatin jihar Jigawa ta bayyana cewa za ta fara biyan ma'aikatan da su ka yi ritaya hakkokinsu da gwamnatin ta rike
  • Hukumar tattara fansho ta jiha da kananan hukumomin Jigawa ta ce an kammala shirin biyan wadanda su ka bar aiki su 1,331
  • Shugaban hukumar, Nasiru Haruna ya bayyana cewa za a biya kudin da yawansu ya kai Naira Biliyan 3.4

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Jigawa - Gwamnatin jihar Jigawa ta ce an fara biyan yan fansho hakkokinsu wadanda su ka ajiye aiki a shekarar da mu ke ciki.

Mutane akalla 1,331 da su ka bar aiki tsakanin Janairu zuwa Yuni 2024 ne za su samu hakkinsu da ya kai Naira Biliyan 3.4.

Kara karanta wannan

Majalisa ta gano inda tallafin buhunan shinkafar Tinubu ke maƙalewa

Jigawa
Za a biya ma'aikatan Jigawa sama da 1000 hakkokinsu Hoto: Legit.ng
Asali: Original

TVC News ta wallafa cewa mukaddashin shugaban hukumar tattara fansho a jihar, Nasiru Haruna ya ce an raba masu karbar fanshon gida hudu. Kashin farko su ne fanshon wadanda su ka ajiye aiki da na wadanda su ka rasu, bashin fanshon wadanda su ka rasu da 8% na kudin da aka hada na fansho.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Jigawa na biyan yan fansho

Gwamnatin jihar Jigawa ta shawarci dukkanin wadanda ke bin gwamnati kudin fansho su fara bin hanyoyin karbar kudadensu da aka fara biya.

Mukaddashin shugaban hukumar fansho a jihar, Nasiru Haruna ne ya bayyana haka, Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa labarin.

Jigawa : Ana hobbasa wajen biyan fansho

Alhaji Nasiru Haruna ya bayyana cewa gwamnatin jihar na kokarin ganin an biya ma'aikatan Jigawa hakkokinsu.

Ya ce zuwa yanzu, gwamnatin jiha ta biya hakkokin ma'aikata da ya kai Naira Biliyan 5.4, kuma an biya dukkanin giratuti da ake bin gwamnati.

Kara karanta wannan

Zamfara: Ana makokin Sarkin Gobir, miyagu sun kwashe mutane, an nemi fansar N50m

Gwamnatin Kano ta fara biyan fansho

A baya mun ruwaito yadda gwamnatin Abba Kabir Yusuf a jihar Kano ta dauko gagarumin aikin biyan ma'aikata hakkokinsu da gwamnatin baya ta gaza biya.

Yayin kaddamar da kashi na biyu na biyan giratuti a jihar, gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da fitar da Naira Biliyan 5 na ma'aikata daga 2016-2019.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.