Kisan Sarkin Gobir Ya Harzuƙa Gwamnatin Tinubu, Minista Ya Ba Sojoji Umarnin Gaggawa

Kisan Sarkin Gobir Ya Harzuƙa Gwamnatin Tinubu, Minista Ya Ba Sojoji Umarnin Gaggawa

  • Gwamnatin tarayya ta umarci rundunar sojojin Najeriya ta farauto waɗanda suka kashe sarkin Gobir a Sakkwato, Muhammad Isa Bawa
  • Karamin ministan tsaro Bello Matawalle ya yi tir da kisan, yana mai cewa dukkan masu hannu a wannan rashin imanin za su ɗanɗana kuɗarsu
  • Matawalle ya ce tsaro shi ne abu na farko da Bola Tinubu ya fi ba fifiko kuma yana bai wa sojoji dukkan goyon bayan da suka bukata

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle ya yi Allah wadai da kisan hakimin Gatawa dake ƙaramar hukumar Sabon Birni a Sakkwato wanda aka fi sani da Sarkin Gobir.

Matawalle ya bayyana kisan sarkin Gobir, Muhammad Isa Bawa a matsayin ɗanyen aiki na rashin imani, inda ya ce duk mai hannu a kisan zai ɗanɗana kuɗarsa.

Kara karanta wannan

Bayan kisan sarkin Gobir, gwamnatin Tinubu ta yi yunkurin kubutar da likitar da aka sace

Bello Matawalle.
Matawalle ya yi tirda kisan sarkin Gobir, ya umarci sojoji su farauto ƴan bindigar da suka aikata wannan ɗanyen aiki Hoto: Bello Matawalle
Asali: Twitter

Yadda 'yan bindiga suka kashe sarkin Gobir

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da Bawa tare da dansa da wasu mutane shida a watan Yuli yayin da suke hanya daga Sokoto zuwa Sabon Birni kusa da bodar Nijar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Punch ta tattaro cewa waɗanda suka tafi kai kuɗin fansar da ƴan bindigar suka nema sun taras da gawar Sarkin Gobir.

Da yake martani kan lamarin a wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na ma'aikatar tsaro ya fitar, Matawalle ya yi tir da kisan basaraken.

Matawalle ya ba hafsun sojoji umarni

Ya kuma umarci sojojin Najeriya su gudanar da bincike tare da farauto ƴan bindigar da suka aikata ɗanyen aiki domin su girbi abin da suka shuka.

A rahoton Channels tv, sanarwar ta ce:

"Karamin Ministan Tsaro ya yi tir da kisan Hakimin Gatawa da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni a Sakkwato, Alhaji Isa Bawa, ya bayyana hakan a matsayin rashin imani."

Kara karanta wannan

Yadda ƴan bindiga suka karɓi kuɗin fansa sama da N50m duk da kashe Sarkin Gobir

"Ya ce kashe basaraken rashin hankali ne kuma ba za a bar makasan su ci bulus ba. Sannan Matawalle ya umarci babban hafsan sojoji ya binciki lamarin don tabbatar da hukunta masu hannu a kisan."

Matawalle ya ƙara da cewa tsaro shi ne babban abin da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sa a gaba, kuma yana ba sojoji duk goyon bayan da suke buƙata.

Yan bindiga sun saki bidiyon mata

A wani rahoton kuma ana cikin jimamin kisan sarkin Gobir, wasu 'yan bindiga sun saki bidiyon mata 26 da suka sace a jihar Neja

'Yan bindigar sun nemi a kai masu babura biyar matsayin fansar duk mace daya, wanda aka kiyasta kudin duk babur kan N2m.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262