Bayan Kashe Sarkin Gobir, 'Yan Bindiga Sun Saki Bidiyon Matan Neja 26 da Suka Sace

Bayan Kashe Sarkin Gobir, 'Yan Bindiga Sun Saki Bidiyon Matan Neja 26 da Suka Sace

  • Ba a gama da jimamin kisan sarkin Gobir, Isa Bawa ba, wasu 'yan bindiga sun saki bidiyon mata 26 da suka sace a jihar Neja
  • 'Yan bindigar sun nemi a kai masu babura biyar matsayin fansar duk mace daya, wanda aka kiyasta kudin duk babur kan N2m
  • Wata mata da ta yi magana a cikin bidiyon, ta shaidawa iyalanta cewa ta samu rauni a kafafuwa, tare da rokon a kai baburan

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Neja - 'Yan bindiga sun saki wani bidiyo mai sosa zuciya na mata kusan 26 da suka sace a garin Allawa da ke karamar hukumar Shiroro, jihar Neja.

Kara karanta wannan

Zamfara: Ana makokin Sarkin Gobir, miyagu sun kwashe mutane, an nemi fansar N50m

A cikin bidiyon, matan sun roki 'yan uwa da abokan arzikinsu da su taimaka su kawo babura 130 da 'yan bindigar suka bukata domin a sake su.

'Yan bindiga sun saki bidiyon matan da suka sace a Neja
'Yan bindiga sun nemi babura 130 domin sakin matan da suka sace a Neja. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

'Yan bindiga sun saki bidiyo

A cikin wani faifan bidiyo da jaridar Daily Trust ta samu, an ga daya daga cikin matan da aka sace daure a jikin bishiya tana fadin bukatun 'yan bindigar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matar wadda ta yi magana da harshen Hausa, ta roki wani dan uwanta mai suna Abdulrahman da ya taimaka ya kawo baburan da aka bukata.

"Umar, don Allah ka yi wa Abdulrahman magana. Sun kawo ni wani waje yanzu, sun ce ba za su sake ni ba sai an kawo abubuwan da suke bukata."

- A cewar matar.

"Na samu rauni a kafa" Inji wata

Matar ta ci gaba da cewa:

"Sun ce in yi magana ta yadda za ku ji muryata kuma ku shaida ni. Na samu rauni a kafafuwana. Don girman Allah da ma'aiki, ku kawo kayan.

Kara karanta wannan

Ana jimamin kisan sarkin Gobir, 'Yan bindiga sun kashe manoma 13 a Arewacin Najeriya

"Sun ce idan kuka kawo kayan, za su sake ni tare da Hajiya. Ina tare da Hajiya a nan."

Wani mazaunin garin Abba Usman ya tabbatar da cewa matan da aka gani a bidiyon na daga cikin mutane 26 da aka yi garkuwa da su a watan Fabrairun bana.

'Yan bindiga sun bukaci babur

Ya ce tuni iyalan matan biyu suka kaiwa 'yan bindiga babura shida, amma yanzu masu garkuwa da mutanen suna neman karin babura kafin a sako matan.

Usman ya kara da cewa iyalan sauran mata 24 sun sanar da ‘yan fashin cewa ba za su iya sayen karin baburan ba.

‘Yan fashin dai na bukatar babura biyar ga kowacce daga cikin matan guda 26, inda kowanne babur ya kai kusan Naira miliyan biyu.

'Yan bindiga sun kashe sarkin Gobir

A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yan bindiga sun kashe sarkin Gobir na Sabon Birni, Alhaji Isa Bawa, bayan shafe sama da kwanaki 20 yana tsare a hannunsu.

Kara karanta wannan

Iyayen marayu, mata sun tsunduma zanga zanga, sun fadi yadda su ke rayuwa a Ondo

An ruwaito cewa wa'adin da 'yan bindigar suka debawa sarkin na kai kudin fansarsa ya kare, abin da ake zargin ya jawo suka kashe shi tare da ci gaba da tsare dansa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.