EFCC Ta Shirya Cafke Tsohon Gwamnan APC, Ta Fadi Matakan da Ta Dauka

EFCC Ta Shirya Cafke Tsohon Gwamnan APC, Ta Fadi Matakan da Ta Dauka

  • Hukumar yaki rashawa ta EFCC ta ce za a gurfanar da Yahaya Bello, tsohon gwamnan jihar Kogi a gaban kuliya
  • Hukumar ta tuhumi Yahaya Bello ne da laifin karkatar da kudi, zagon kasa da kuma sama da fadi da kimanin da N80bn
  • Dele Oyewale, kakakin EFCC ya bayyana cewa hukumar ta nemi taimakon jami'an tsaron gida da waje domin kama Yahaya Bello

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Babbar hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya (EFCC) ta yi magana kan cafke tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.

EFCC ta ce tana aiki da hukumomi na cikin gida da na waje domin ganin an gurfanar da tsohon gwamnan gaban kuliya.

Kara karanta wannan

Dan uwan Kwankwaso ya gaza cika sharadin beli, PCACC ta ci gaba da tsare shi

Hukumar EFCC ta yi magana kan kama Yahaya Bello
EFCC ta nemi taimakon jami'an tsaron cikin gida da na waje domin kama Yahaya Bello. Hoto: @OfficialGYBKogi
Asali: Facebook

Yahaya Bello na 'yar buya da EFCC

Jaridar Daily Trust ta ruwaito EFCC ta tuhumi Yahaya Bello da laifuka 19 da suka shafi karkatar da N80bn,daga asusun gwamnatin jihar Kogi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai tun daga lokacin da hukumar ta shigar da karar ba ta samu damar gurfanar da shi gaban kotu ba saboda ta gaza kama shi.

Tsohon gwamnan ya ki halartar zaman kotu guda shida da aka shirya domin gurfanar da shi yayin da har yanzu ba a gano inda ya ke buya ba.

Hukumar EFCC ta shirya kama Yahaya Bello

Da take magana game da ci gaban, hukumar EFCC ta dage cewa za a gurfanar da Yahaya Bello a gaban kuliya.

Shugaban sashen yada labarai na EFCC, Dele Oyewale, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin wata tattaunawa da ya yi da maneman labarai, inji The Cable.

Kara karanta wannan

Ba a gama da kwangilar magani ba, gwamnatin Kano ta bankado badakalar N660m

Yayin da yake bayyana cewa kotun ta kara daukaka matsayin hukumar, Oyewale ya ce hukumar na hada kai da jami’an tsaro na cikin gida da na waje domin tabbatar da kama Bello.

“A yanzu da nake magana, Yahaya Bello ya zama wanda ake nema ruwa a jallo. Mun hada kai da jami'an tsaro na cikin gida da na waje domin kama shi."

- A cewar Oyewale.

Shugaban EFCC zai yi murabus?

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede, ya sha alwashin bin diddigin badakalar rashawa ta tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello.

Mista Olukoyede ya kuma lashi takobin cewa zai yi murabus daga mukamin shugaban EFCC ma damar ba a gurfanar da tsohon gwamnan a gaban kotu ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.