Akalin Alkalan Najeriya Ya Bar Aiki a Gwamnati, Bayanai Sun Fito
- Babban alkalin Najeriya (CJN) Mai shari'a Olukayode Ariwoola ya yo ritaya daga aiki bayan cika shekara 70 a duniya kamar yadda doka ta tanada
- Mai shari'a Ariwoola ya zama alkalin alkalan Najeriya ne a watan Yuni, 2022 bayan magabacinsa, Tanko Muhammad ya yi murabus
- Ana raɗe-raɗin dai shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu na shirin ɗauko shugaban alkalan jihar Legas, Mai shari'a Kudirat Kekere-Ekun ta maye gurbin CJN
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Alkalin Alƙalan Najeriya (CJN) na 22, Mai Shari'a Olukayode Ariwoola ya yi ritaya daga aiki bayan cika shekaru 70 kamar yadda doka ta tanada.
An haifi Mai shari’a Ariwoola a ranar 22 ga Agusta, 1954, ma'ana dai a yau Alhamis yake cika shekaru 70 a duniya.
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa ajiye aikin Alkalin Alƙalai na 22 a tarihi ya kawo ƙarshen dogon lokacin da Ariwoola ya shafe yana yi wa ɓangaren shari'a hidima.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Taƙaitaccen bayani kan CJN mai ritaya
A ranar 22 ga watan Nuwamban, 2011, Mai Shari'a Ariwoola ya zama ɗaya daga cikin alkalan da ke zama a kotun ƙolin Najeriya.
Daga bisani kuma ya zama babban alkalin Najeiriya (CJN) a ranar 27 ga watan Yuni, 2022, bayan murabus din wanda ya gabace shi, Mai Shari'a Tanko Muhammad.
Majalisar dattawan Najeriya ta tabbatar da nadinsa a matsayin CJN a ranar 21 ga Satumba, 2022, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Tun lokacin da aka fara surutu kan batun ajiye aikin CJN a watan Agusta, alamu sun nuna da yiwuwar Mai Shari'a Kudirat Kekere-Ekun ta zama magajinsa.
Ana raɗe-raɗin dai shugabar alƙalan ta jihar Legas, Mai Shari'a Kudirat na iya zama wacce za a naɗa ta zama sabuwar shugabar alkalan Najeriya.
Gwamnati ta ji koken ƴan Najeriya
A wani rahoton kuma gwamnatin tarayya ta bayyana cewa zanga-zangar da aka yi ta ƙara tunatar da ita bukatar ta riƙa sauraron koken jama'a.
Ministan kasafin kuɗi da tsare-tsaren kasa ya ce a yanzu gwamnati na zama ta saurari koken ƴan Najeriya fiye da a baya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng