Yan Kwadago Sun ba Tinubu Mafita kan Wahalar Mai a Najeriya

Yan Kwadago Sun ba Tinubu Mafita kan Wahalar Mai a Najeriya

  • Kungiyar kwadago ta bayyana kuskuren gwamnatin tarayya da ya jefa al'umma cikin wahala da tsadar man fetur a fadin Najeriya
  • Shugaban kungiyar TUC, Festus Osifo ya ce har yanzu gwamnatin tarayya ba ta dauko hanyar shawo kan wahalar man fetur ba
  • Hakan na zuwa ne kwanaki biyu bayan rundunar yan sanda ta kasa ta gayyaci shugaban yan kwadagon NLC, Joe Ajaero

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Ƙungiyar kwadago ta TUC ta bayyana abin da ya hana kawo ƙarshen wahalar man fetur a fadin Najeriya.

Shugaban kungiyar TUC, Festus Osifo ya ce matsalar ta shafi gaza samar da hanyoyin wadatar da jihohin Najeriya man fetur a saukake.

Kara karanta wannan

Batun tsige Akpabio: Kungiyar tsofaffin tsagerun Neja Delta ta yi gargadi

Gida mai
Yan kwadago sun ba Tinubu shawara kan tsadar mai. Hoto
Asali: Getty Images

Jaridar Premium Times ta wallafa cewa shugaban TUC ya buƙaci a dawo tura man fetur ta bututun mai da aka birne a ƙarƙashin ƙasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin wahalar mai a Najeriya

Shugaban kungiyar TUC, Festus Osifo ya ce rashin isassun hanyoyin tura man fetur jihohi na cikin matsalolin da suke jawo wahalar man fetur a Najeriya.

Festus Osifo ya ce matuƙar gwamnatin tarayya ba ta dauki matakin samar da hanyoyin saukaka tura man fetur ba da wahala a kawo karshen matsalar.

Osifo ya ce idan ba a dauki matakin da ya dace ba to ko da an fita daga matsalar a nan gaba kadan za a sake dawowa kamar yadda ake ta fama tsawon shekaru.

Gyara wuraren ajiye mai a jihohi

Rahoton Channels Television ya nuna cewa shugaban TUC ya kara da cewa gwamnatin Najeriya tana da wuraren ajiye mai a jihohi har guda 21.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi zazzafan martani ga Shugaba Tinubu kan dawo da tallafin man fetur

Ya ce a da wuraren suna aiki, abin da ya kamata shi ne da tun da dadewa an magance matsalar wahalar mai a Najeriya.

Haka zalika Festus Osifo ya ce akwai bukatar gwamnatin tarayya ta dawo da tura man fetur ta bututun da aka birne a ƙarƙashin ƙasa zuwa jihohi.

An ba Tinubu shawara kan tallafin mai

A wani rahoton, kun ji cewa tsohuwar ministar ilimi, Dakta Oby Ezekwesili ta shiga sahun waɗanda suka yi magana a kan cire tallafin mai.

Oby Ezekwesili ta ce cire tallafi kawai ba zai kawo sauyi a tattalin Najeriya ba har sai shugaban kasa ya kara daukan wasu matakai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng