Ana Jimamin Kisan Sarkin Gobir, 'Yan Bindiga Sun Kashe Manoma 13 a Arewacin Najeriya

Ana Jimamin Kisan Sarkin Gobir, 'Yan Bindiga Sun Kashe Manoma 13 a Arewacin Najeriya

  • 'Yan bindiga sun yi sanadiyyar ajalin manoma 13 a karamar hukumar Shiroro da ke jihar Neja a lokacin da suke aikin gonarsu
  • Shugaban karamar hukumar, Hon. Akilu Isyaku, ya tabbatar da kashe manoman a ranar Laraba tare da bayar da karin bayani
  • Wannan harin na zuwa ne awanni bayan da wasu 'yan bindiga suka kashe sarkin Gobir, Isa Bawa kwanaki bayan garkuwa da shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Neja - Wasu ‘yan bindiga sun kashe manoma 13 a gonakinsu da ke garin Ijuwa a yankin Alawa na karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja.

Shugaban karamar hukumar, Akilu Isyaku, ya tabbatar da kashe manoman 13 a wata hira da ya yi da wani gidan rediyo a Minna ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi martani mai zafi kan mutuwar Sarkin Gobir, ya fadi laifin gwamnatin Tinubu

'Yan bindiga sun kashe manoma 13 a karamar hukumar Shiroro, jihar Neja
Neja: 'Yan bindiga sun kashe manoma 13 a yankin Alawa. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

'Yan bindiga sun kashe manoma

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito shugaban karamar hukumar ya bayyana cewa 'yan bindigar sun kashe mutum tara a lokaci daya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hon. Akilu Isyaku ya kuma bayyana cewa 'yan ta'addan sun kashe karin manoma hudu a wani wuri na daban, amma duka a rana daya.

Hakazalika, wata majiya ta bayyana cewa 'yan bindigar sun farmaki kauyen Ijuwa ne bisa zargin mutanen garin na kaiwa jami'an tsaro kwarmato kan ayyukansu.

Gwamnatin Neja ta yi martani

A halin da ake ciki, mukaddashin gwamnan jihar Neja, Yakubu Garba ya bayyana harin a matsayin 'harin shaidanci' da kuma rashin tausayi.

Garba a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya jajantawa iyalan wadanda aka kashe, al'ummar Ijuwa da ma daukacin karamar hukumar Shiroro bisa abin da ya faru.

An tattaro cewa wasu manoma da dama da ke nesa da inda harin ya faru sun bar gonakinsu saboda fargabar harin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai farmaki, sun yi garkuwa da daliban kwalejin kiwon lafiya

'Yan bindiga sun kashe sarkin Gobir

A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yan bindiga sun kashe sarkin Gobir na Sabon Birni da ke a jihar Sokoto, Alhaji Isa Bawa yayin da suke ci gaba da tsare dansa.

An ruwaito cewa basaraken ya shafe sama da kwanaki 20 a hannun 'yan bindigar wadanda suka nemi kudin fansar kusan N500m domin sakinsa da wani dansa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.