Bayan Kashe Sarkin Gobir, Yan Bindiga Sun yi Barazana ga Ɗalibai Likitoci 20 a Arewa

Bayan Kashe Sarkin Gobir, Yan Bindiga Sun yi Barazana ga Ɗalibai Likitoci 20 a Arewa

  • Al'umma na cigaba da nuna damuwa kan wasu ɗalibai likitoci 20 da aka sace a Benue yayin da suka dauko hanya zuwa jihar Enugu
  • Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia ya umurci jami'an tsaro kan yin duk abin da ya dace domin samun kubutar da dalibai likitocin
  • Haka zalika sufeton yan sanda na kasa, IG Kayode Egbetokun ya ba jami'an tsaro umurnin binciko halin da ake ciki da ceto daliban

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Benue - Dalibai likitoci da aka sace a jihar Benue sun shafe mako guda bayan sun bata ba tare da gano inda suke be.

Al'umma sun nuna damuwa ganin abin da ya faru da mai martaba sarkin Gobir a hannun masu garkuwa da mutane.

Kara karanta wannan

Abubuwa 6 da ya kamata ku sani kan marigayi Sarkin Gobir da masarautarsa

Jihar Benue
Likitoci 20 sun shafe mako da bata a Benue. Hoto: Legit
Asali: Original

Jaridar Daily Trust wallafa cewa ana raɗe radin cewa yan bindigar da suka kama daliban sun bukaci kudin fansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maganar kama likitoci a Benue

A ranar Alhamis da ta wuce aka kama dalibai likitoci su 20 a jihar Benue suna kan hanyar zuwa Enugu domin halartar wani taro.

Legit ta ruwaito cewa ɗaliban sun fito ne daga jami'o'in Maiduguri da Filato inda suke karatun likitanci.

Masu garkuwa sun yi barazana ga dalibai

Leadership ta wallafa cewa masu garkuwa da daliban sun bukaci a ba su kudin fansa N50m kafin su sake su.

Haka zalika masu garkuwa da mutanen sun ce za su cutar da daliban matuƙar ba a biya musu bukatunsu a kan lokaci ba.

Neman karin haske wajen yan sanda

Maneman labarai sun yi kokarin tuntubar rundunar yan sandan jihar Benue domin jin halin da ake ciki kan lamarin.

Kara karanta wannan

Ana shirin zanga zanta ta 2, an gano halin da ake ciki bayan kifar da gwamnatin Bangladesh

Sai dai zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, kakakin rundunar yan sanda a jihar, SP Catherine Anene ba ta yi martani kan sakon da aka tura mata ba.

Sojoji sun yi artabu da yan bindiga

A wani rahoton, kun ji cewa an yi artabu tsakanin sojoji da 'yan bindiga a garin Gudiri da ke gundumar Bashar a karamar hukumar Wase.

Rahotanni sun ce an kashe ‘yan bindiga da dama da kuma wasu sojoji yayin artabun da suka yi a kokarin sojojin na yaki da ta'addanci a Filato.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng