Atiku Ya Yi Martani Mai Zafi kan Mutuwar Sarkin Gobir, Ya Fadi Laifin Gwamnatin Tinubu

Atiku Ya Yi Martani Mai Zafi kan Mutuwar Sarkin Gobir, Ya Fadi Laifin Gwamnatin Tinubu

  • Atiku Abubakar ya ce halin ko in kula da gwamnati ke nunawa da rashin ingantattun tsare-tsare ya kara lalata tsaro
  • 'Dan takarar shugaban kasar a 2023 a karkashin PDP ya ce kisan gillar da aka yi wa sarkin Gobir alama ce ta gwamnati ta gaza
  • Kafin maganar Atiku, shugaba Bola Tinubu ya mika sakon ta'aziyyar mutuwar basaraken tare da ba da tabbacin inganta tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Sokoto - Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya ya yi magana kan kisan gillar da 'yan bindiga suka yiwa Sarkin Gobir, Alhaji Isa Bawa.

An ce 'yan bindigar sun kashe sarkin Gobir, wanda kuma shi ne hakimin Gatawa da ke Sabon Birni a jihar Sokoto bayan shafe sama da kwanaki 20 a hannunsu.

Kara karanta wannan

"Za mu dauki mataki": Tinubu ya yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa Sarkin Gobir

Atiku Abubakar ya yi magana kan kisan gillar da aka yiwa sarkin Gobir
Atiku ya zargi gwamnatin tarayya da sakaci bayan mutuwar sakin Gobir. Hoto: Atiku Abubakar, Abbakar Ai
Asali: Facebook

Atiku ya magantu kan kisan sarkin Gobir

A cikin sakon ta'aziyya da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Laraba, Atiku ya ce sakacin gwamnati na nuna damuwa da daukar matakai ya ta'azzara matsalar tsaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Atiku:

"Ina mika sakon ta'aziyyata ga iyalai, al'ummar masarautar Gobir da gwamnatin jihar Sakkwato bisa wannan babban rashi na mai martaba Alhaji Isa Bawa.
"Mummunan ta'addancin da 'yan bindigar suka aikata wanda ya haifar da mutuwar irin wannan shugaba abin tunatarwa ne.
"Babban abin tunatarwa ne game da matsananciyar bukatar inganta matakan tsaro wajen kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa."

Atiku ya ga laifin gwamnatin Tinubu

A cikin sakon ta'aziyyar, tsohon dan takarar shugaban kasar ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da yin sakaci kan lamuran tsaron kasar.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce:

Kara karanta wannan

Abubuwa 6 da ya kamata ku sani kan marigayi Sarkin Gobir da masarautarsa

"Gazawar gwamnati wajen nuna damuwa ko samar da ingantattun dabarun tsaro ya taimaka wajen kara ta'azzara al'amuran tsaro a cikin 'yan kwanakin nan.
"Yana da mahimmanci a nanata cewa dole ne gwamnati ta samar da tsaro wanda zai tabbatar da kare rayukan jama'a.
"Gwamnati ta dauki matakan da za su ba 'yan kasar damar yin rayuwa ba tare da fargabar fadawa komar 'yan ta'adda ba."

Duba sakon Atiku a nan kasa:

Tinubu ya magantu kan mutuwar sarkin Gobir

A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu ya yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa Sarkin Gobir, Alhaji Isa Bawa yana mai jaddada cewa za a mayar da martani.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Cif Ajuri Ngelale ya fitar, Tinubu ya aika sakon ta'aziyya ga iyalan basaraken, masarautar Gobir da gwamnatin Sokoto.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.