Bayan Sayen Jirgi, An Tono yadda Tinubu Ya Kashe sama da N2.3bn wajen Tafiye Tafiye

Bayan Sayen Jirgi, An Tono yadda Tinubu Ya Kashe sama da N2.3bn wajen Tafiye Tafiye

  • Masana tattali sun fara kokawa kan yadda shugaba Bola Ahmed Tinubu yake kashe makudan kudi a lokacin tafiye-tafiye zuwa ketare
  • Ƙididdiga ta tabbatar da cewa a cikin wata shida kawai gwamnatin tarayya ta kashe kudi har Naira 2.3 biliyan a harkar tafiye tafiye
  • Tafiye-tafiyen shugaban kasa na daukan hankula ne kasancewar shugabanni na kukan babu kudi kuma suna rokon cewa a kara hakuri

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Masana sun yi kididdiga kan yadda gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ke kashe kudi da sunan tafiye tafiyen zuwa kasashe.

A cikin watanni shida, shugaba Bola Tinubu ya kashe sama da Naira biliyan 2 a harkar tafiye tafiye.

Kara karanta wannan

Zaben Kano: NNPP ta tanadin katin WAEC da NECO, za a duba takardun karatun yan takara

Tinubu a jirgi
Tinubu ya kashe makudan kudi a tafiye tafiye. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Business Day ta wallafa cewa a cikin shekara daya Bola Tinubu ya ziyarci kasashe 10 inda ya ƙashe sama da Naira biliyan 3.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya kashe N2.3bn a tafiye tafiye

Ƙididdiga ta tabbatar da cewa daga 21 ga Fabrairu zuwa 19 ga Yuli shugaba Tinubu ya kashe kudi N2.3b a tafiye tafiye.

An ruwaito cewa fadar shugaban kasa ta ware N300m kan tafiye tafiyen Tinubu na watan Janairu.

Wasu ƙasashen da Tinubu ya je

Daga watan Fabrairu zuwa Maris Bola Tinubu da mataimakinsa sun kashe makudan kudi zuwa kasashen Switzerland, Liberia, Franc, Côte d’Ivoire da sauransu.

Daily Trust ta wallafa cewa a ranar 24 ga watan Fabrairu, gwamnatin tarayya ta kashe N750m domin sayen daloli yayin tafiyar shugaban kasa zuwa Dubai.

Tafiyar Tinubu kasar Faransa a Agusta

A ranar Litinin shugaba Tinubu ya kara tafiya kasar Faransa a sabon jirgin shugaban kasa da aka saya masa wanda ana ganin za a kara kashe kudi sosai.

Kara karanta wannan

Jam'iyyun adawa sun hada kai, sun ragargaji Tinubu kan sayen sabon jirgi

Sai dai a wannan karon gwamnatin tarayya ta ce za ta rage kudin da ake kashewa wajen tafiye tafiyen shugaban kasar

Oby ta ba Tinubu shawara kan tattali

A wani rahoton, kun ji cewa tsohuwar ministar ilimi, Oby Ezekwesili ta shiga sahun waɗanda suka yi magana a kan cire tallafin fetur da Bola Tinubu ya yi.

Oby Ezekwesili ta ce cire tallafi kawai ba zai kawo sauyi a tattalin Najeriya ba har sai shugaban kasa ya kara daukan wasu matakai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng