Yadda Ƴan Bindiga Suka Karɓi Kuɗin Fansa Sama da N50m duk da Kashe Sarkin Gobir
- Ƴan bindiga sun karbi N60m da babura biyar gabanin sako ɗan marigayi Sarkin Gobir a jihar Sakkwato a Arewa maso Yamma
- Wannan dai na zuwa ne bayan ɓarayin dajin sun kashe sarkin na Gobir, Isa Muhammad Bawa wanda suka yi garkuwa da shi
- Labarin kashe basaraken dai ya girgiza kusan ko ina a yankin Arewa, bayanai sun nuna ƴan bindigar sun biene gawarsa a jeji
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Sokoto - Bayan mutuwar sarkin Gobir a hannun masu garkuwa, ƴan bindigar sun sako ɗansa da ke tsare a hannunsu bayan sun karɓi kuɗin fansa.
Idan ba ku manta ba ƴan bindiga sun kashe sarkin Gobir, Isa Muhammad Bawa, wanda suka yi garkuwa da shi tare da ɗansa kwanaki 25 da suka gabata.
Babban ɗan marigayi sarkin, Surajo Isa ne ya tabbatar da hakan ga jaridar Daily Trust a daren ranar Laraba, 21 ga watan Agusta, 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sarkin Gobir: Yadda ɓarayi suka karɓi kuɗi
Ya ce barayin jajin sun karbi Naira miliyan 60 kuma an ba su babura biyar kamar yadda suka bukata domin su sako su.
"Waɗanda suka je kai kuɗin sun dawo daga wurin 'yan bindigar da misalin karfe 8:30 na dare," in ji Surajo.
Surajo Isa ya ƙara da cewa ƴan bindigar sun birne mahaifinsu, sarkin Gobir bayan Allah ya masa rasuwa a hannunsu, rahoton Leadership.
Ɗan sarkin Gobir ya kuɓuta
Da yake tabbatar da lamarin, Hon. Aminu Boza, dan majalisar dokokin jihar Sokoto, ya ce yanzu haka ɗan marigayi Sarkin na jinya a asibitin koyarwa na Usman Danfodio.
Aminu Boza ya ce:
"Sai dai abin takaicin sun binne gawar marigayi sarki a daji, labari ya zo mana cewa sun binne shi da safe.
"Shi kuma ɗan marigayin, Alhaji Kabir Isa, wanda aka sace su tare ya kubuta, yana asibitin koyarwa na Usman Danfodio (UDUTH) ana duba lafiyarsa. Babban abin takaici shi ne ba za a sake ganin Sarkin ba.
Gwamnatin Sokoto za ta kakkaɓe ƴan bindiga
A wani rahoton kuma gwamnatin jihar Sokoto ta fara ɗaukar matakan kawo ƙarshen ayyukan ƴan bindiga a ƙaramar hukumar Tureta ta jihar.
Gwamna Ahmed Aliyu ya amince da gina titin hanya wanda zai ba jami'an tsaro damar zuwa maɓoyar ƴan bindiga.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng