Ana cikin Rudani kan Tallafin Mai, Tsohuwar Minista Ta ba Tinubu Mafita

Ana cikin Rudani kan Tallafin Mai, Tsohuwar Minista Ta ba Tinubu Mafita

  • Tsohuwar ministar ilimi, Dakta Oby Ezekwesili ta shiga sahun waɗanda suka yi magana a kan cire tallafin fetur da Bola Tinubu ya yi
  • Oby Ezekwesili ta ce cire tallafi kawai ba zai kawo sauyi a tattalin Najeriya ba har sai shugaban kasa ya kara daukan wasu matakai
  • Tsohuwar ministar ta bukaci gwamnatin tarayya ta canza tsarin gudanarwar kamfanin NNPCL domin kawo cigaba a harkar mai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohuwar ministar Ilimi ta kasa, Dakta Oby Ezekwesili ta ba shugaban kasa shawara bayan cire tallafin man fetur.

Dakta Oby Ezekwesili ta ce gwamnatin tarayya ba ta bi hanyar da za a samu cigaba a Najeriya ba wajen cire tallafin man fetur.

Kara karanta wannan

"Ba zai iya ba," Malami ya buƙaci Shugaba Tinubu ya tsige Minista 1 nan take

Oby Ezekwesili
An ba Tinubu shawara kan cire tallafin man fetur. Hoto: Oby Ezekwesili|Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Tsohuwar ministar ta yi bayani ne a wata hira da ta yi a gidan Talabijin din Channels kan harkar tattalin Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Oby Ezekwesili kan cire tallafin man fetur

Tsohuwar ministar ilmin ta ce akwai bukatar gwamnatin tarayya ta sake nazari bayan cire tallafin man fetur da ta yi.

Dakta Oby Ezekwesili ta yi magana ne kan yadda aka shekara guda ba tare da yan Najeriya sun fara ganin fa'idar cire tallafin man fetur ba.

Wane tsari ya kamata Tinubu ya bi?

Dakta Oby Ezekwesili ta ce cire tallafin man fetur kawai da Tinubu ya yi ba zai kai Najeriya zuwa tudun-na-tsira ba.

Ezekwesili ta ce akwai bukatar gwamnatin tarayya ta mika ragamar gudanar da NNPCL ga yan kasuwa domin saukaka lamura.

Tsohuwar ministar ta ce kamar yadda gwamnatin baya ta cefanar da kamfanin sadarwa na NITEL aka samu sauki a fannin, hakan ya kamata a yi a harkar man fetur.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya nemi hakkin 'yan kasa, ya bukaci bayanan sabon jirgin Tinubu

Maganar tsadar rayuwa a Najeriya

Haka zalika tsohuwar ministar ta yi magana kan yadda ake shan wahalar rayuwa a Najeriya amma yan siyasa na cigaba da fantamawa.

Oby Ezekwesili ta ce akwai rashin tausayi kan halin da yan siyasar suke nunawa kuma ya kamata su canza, tana zarginsu da barna.

Waziri Adio ya yi maganar tallafin mai

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban NEITI, Waziri Adio ya bukaci kamfanin NNPCL ya fito fili ya yi bayani dalla dalla kan tallafin mai.

Waziri Adio ya ce akwai lauje cikin nadi kan yadda NNPCL yake kauce-kauce wajen bayanin maido da tallafin man fetur a Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng