Bacin Ciki: Jihohin Najeriya 6 da Mutane 43 Suka Rasa Rayukansu Daga Cin Abinci

Bacin Ciki: Jihohin Najeriya 6 da Mutane 43 Suka Rasa Rayukansu Daga Cin Abinci

An samu rahotannin mutane da dama da suka rasa rayukansu bayan sun ci gurbataccen abinci a wasu jihohin kasar nan, lamarin da ya tayar da hankulan jama'a.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

A kidaya ta karshe, an ce wadanda suka mutu sakamakon cin abinci da ya gurbace a fadin kasar sun kai 43 yayin da wasu da dama ke kwance a asibiti.

Kimanin mutane 34 suka mutu a jihohi 6 bayan sun ci abinci mai guba
an shiga fargaba yayin da mutane 43 suka mutu sanadin cin abinci mai guba. Hoto: Kypros
Asali: Getty Images

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mutane sun fara fargaba game da abincin da ake ci, da tunanin ko gurbacewar sinadari da kuma yanayin tsaftar da ake sarrafa abinci ne sila.

Wannan lamari ya sanya ma'aikatan kiwon lafiyar jama'a, masana abinci mai gina jiki da sauran masu ruwa da tsaki sun dukufa ba da shawarar ka'idojin sarrafa abinci da tsabta.

Kara karanta wannan

Amurka ta cafke dan Najeriya kan zambar $10m, yana fuskantar daurin shekara 20

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jerin jihohin da abinci ya kashe mutane

1. Mutane 8 sun mutu a Kwara

A makon da ya gabata, a unguwar Eruda da ke karamar hukumar Ilorin ta Yamma a jihar Kwara, wata mata mai shekaru 70 da danta mai shekaru 34 da jikoki biyu sun rasu.

An ruwaito cewa 'yan gida dayan sun mutu ne jim kadan bayan sun ci amala, wanda ake kyautata zaton tana dauke da sinadari mai guba.

A makon nan muka ruwaito a unguwar Oshin da ke Asa Dam a Ilorin, wata matar aure da ‘ya’yanta uku, wadanda ba su wuce shekara 10 ba, sun mutu bayan sun ci shinkafa.

2. Mutum 5 sun mutu a Anambra

A farkon watan nan ne aka tabbatar da mutuwar wasu yara hudu da mahaifiyarsu sakamakon cin guba a unguwar Abubor Nnewichi da ke Nnewi ta Arewa a jihar Anambra.

Kara karanta wannan

An cafke masu kaiwa 'yan bindiga makamai a Arewa, 'yan sanda sun yi bayani

3. An rasa mutane 12 a Sokoto

Har ila yau, a jihar Sokoto, an ruwaito cewa wasu 'yan gida daya su bakwai sun mutu bayan sun ci rogo a kauyen Runjin Barmo da ke gundumar Kajiji a karamar hukumar Shagari.

A ranar Lahadin da ta gabata, a karamar hukumar Shagari ta Sakkwato, aka kara samun mutum biyar daga cikin mutane bakwai sun mutu bayan da suka ci abinci da gishirin lalle.

Da take tabbatar da faruwar lamarin, kwamishiniyar lafiya ta jihar, Asabe Balarabe, ta ce lamarin ya faru ne a kauyen Kaurar Wanke.

4. 'Yan gida daya sun mutu a Nasarawa

An samu makamancin abin da ya faru a Sokoto a jihar Nasarawa, inda a mako kusan biyu da suka gabata mutane shida ‘yan gida daya suka mutu a unguwar Gidinye.

An ce mutanen sun mutu ne bayan sun gama cin abinci da ake kyautata zaton akwai mugun sinadari a ciki, a Gidinye da ke karamar hukumar Obi.

Kara karanta wannan

Tsohon mataimakin shugaban majalisa ya yanke jiki ya fadi matacce, bayanai sun fito

5. Uwa da 'ya'ya 5 sun mutu a Kano

A Kano, an rahoto cewa wata uwa da ’ya’yanta biyar sun mutu sakamakon ciwon ciki, bayan sun ci wani abinci a kauyen Karkari da ke karamar hukumar Gwarzo ta jihar.

Wani rahoto ya ce wadanda suka mutun sun ci dan wake ne da aka hada shi da garin rogo da lalatacce sakamakon rashin kudin da matar za ta iya sayawa yaran abinci.

6. An birne gawar mutum 5 a Kogi

Kwanaki kadan da suka gabata, gwamnatin jihar Kogi ta sanar da cewa mutane shida sun mutu bayan sun ci amala.

Gwamnatin ta ce ana zargin amala da suka ci ya lalace ne a wani gida a unguwar Anyoke dake unguwar Okunchi a karamar hukumar Adavi ta jihar.

Mutane sun mutu daga cin abinci

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin jihar Cross River ta sanar da cewa mutane da dama sun mutu a karamar hukumar Abi ta jihar bayan cin abinci.

Kara karanta wannan

Miyagu na yi wa jami'an tsaro dauki ɗai ɗai, an kona wani har gida a Katsina

Gwamnatin ta ce jami'an taimakon gaggawa ciki har da na Red Cross da na hukumar yaki da annoba da ma'aikatar lafiya sun kai daukin gaggawa domin kai dauki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.