'Yan uwa 3 sun sheka barzahu bayan sun kwashi garar Amala a Ilorin
- Yara uku 'yan gida daya sun sheka barzahu bayan kwasar garar Amala da suka yi
- An gano cewa yara biyar ne suka ci abincin amma sai uku suka fara amai kuma aka tafi dasu asibiti
- An bi bayansu da sauran biyun amma sai uku suka ce ga garinku, biyun kuwa sun wartsake bayan taimakon likitoci
Ilorin, Kwara
'Yan gida daya har mutum uku sun rasu a jihar Kwara bayan sun ci guba. An gano cewa sun rasa rayukansu ne sakamakon cin Amala da suka yi a karamar hukumar Ilorin ta gabas.
Daily Trust ta ruwaito cewa 'yan uwa biyar ne suka ci abincin. Tuni aka kwashesu zuwa asibuti dake Igboro inda aka tabbatar da mutuwar uku daga ciki.
KU KARANTA: Luguden wuta: Sojoji sun sheke 'yan bindiga 120 a dajin Sububu dake Zamfara
KU KARANTA: N700m na rashawar Diezani: EFCC ta sake gurfanar da Yero tare da sauran
Karin Bayani: 'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Mai Sanda Mai Daraja Ta Ɗaya, Sun Nemi Maƙuden Kuɗi Na Fansa
Wannan na zuwa ne bayan kusan wata daya da irin hatsarin cin guba ya auku a yankunan Baruteen da Kaiama dake karamar hukumar Kwara ta arewa. Rayuka 17 ne suka salwanta sakamakon hakan.
A yayin da aka tuntubi kakakin NSCDC, Babawale Zaid Afolabi ya ce bai san da aukuwar lamarin ba.
Jami'in DSNO ya tabbatar
Amma jami'in kula da barkewar cutuka na jihar Kwara, Alhaji Muhammad Abdullahi ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya kara da cewa an sallami sauran mutum biyun daga asibiti.
Ya ce: "Lokacin da muka isa wurin, mahaifinsu ya sanar da mu cewa biyar daga cikin 'ya'yansa sun ci amala amma uku daga ciki sun fara amai kafin a mika su asibitin kwararru dake Ilorin.
"Ya ce yayin da suke fama, an sake kai daya wani asibitin amma an tabbatar da mutuwar ukun farko.
"Mahaifinsu wanda manomi ne ya sanar damu cewa da kanshi ya noma doyar da aka yi garin amalan kuma ba zai iya cewa ga abinda ya faru ba," ya kara da cewa.
DSNO din yace sauran yaran biyu sun wartsake a yayin da suka gansu a ranar Talata, Daily Trust ta ruwaito.
A wani labari na daban, luguden wutan da jiragen yakin sojin saman Najeriya suka yi wa 'yan bindiga ya hada da ran wata mata tare da 'ya'yanta hudu a Sububu dake jihar Zamfara.
Majiyoyi daban-daban sun sanar da Daily Trust cewa jiragen yakin NAF sun tsinkayi dajin Sububu tsakanin kananan hukumomin Shinkafi da Maradun yayin da mugun lamarin ya faru.
Dajin Sububu shine yanzu babbar maboyar 'yan bindiga a jihar Zamfara. Daga dajin suke kaddamar da hari kan matafiya a babban titin Sokoto zuwa Gusau da kuma kauyukan jihohin Sokoto da Zamfara.
Asali: Legit.ng