1998: Yadda Tinubu Ya Sauya Rayuwar Sufeta Janar na Ƴan Sandan Najeriya cikin Awa 24
- Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, IGP Kayode Egbetokun ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ne ya canja rayuwarsa
- Kayode Egbetokun ya ce haduwarsa da Tinubu a shekarar 1998 ta sauya rayuwarsa da ta aikinsa gaba daya, abin da ba zai manta ba
- Sufeta janar na 'yan sandan ya bayyana hakan ne a yayin da ake kaddamar da wani littafi da ya shafi aikin 'yan sanda da zaman lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Sufeta Janar na 'yan sandan Najeriya (IGP) Kayode Egbetokun ya ba da labarin yadda haduwarsa da shugaba Bola Tinubu ta canja rayuwarsa.
IGP Egbetokun wanda ya tariyo haduwarsa da shugaban a shekarar 1998 a wajen kaddamar da wani littafi ya ce Tinubu ya sauya rayuwarsa a cikin awa 24.
Rahoton Arise News ya bayyana cewa taken littafin da shugaban 'yan sanda ya halarci kaddamarwa shi ne: "Karatu a aikin 'yan sanda, zaman lafiya da tsaro."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Yadda Tinubu ya canja rayuwata" - Egbetokun
A cewar IGP Egbetokun:
"Dole ne in tuno da tasirin wani mutum a rayuwata da aiki na. Na hadu da Shugaba Bola Tinubu a 1998, kuma haduwar ta kawo sauyi mai kyau a rayuwata cikin sa’o’i 24.
“Yayin da nake tsaye a nan yau, bakina na cike da son bayyana nasororin rayuwata da yiwa Ubangiji godya. Amma tun da taron ba na haka ba ne, zan jinkirta zuwa wani lokaci."
An ruwaito cewa littafin wata karramawa ce ga shugaban 'yan sandan, lamarin da ya ce nasararsa daga Ubangiji ce da kuma taimakon Shugaba Tinubu.
Tinubu ya jinjinawa kokarin sufeta
Shugaba Bola Tinubu wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume a wajen kaddamar da littafin, ya ce littafin ya dace da shugaban 'yan sandan.
Tinubu ya kuma ce sadaukarwar Egbetokun na bin doka da yin adalci, wanzar da zaman lafiya da tsaro ya bar tarihi maras gogewa a fagen aikin 'yan sanda, inji rahoton Vanguard.
Tinubu ya kammala da cewa IGP Egbetokun na daya daga cikin jiga-jigan da suka yi tsayin daka da sadaukar da komai nasu domin tabbatar da tsaron kasarmu.
Shugaba Tinubu ya dora Egbetokun kujerar IGP
A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaba Bola Tinubu, a watan Yunin 2023 ya amince da nadin Kayode Egbetokun a matsayin Sufeta Janar na rundunar 'yan sandan Najeriya.
Sanarwar amincewa da nadin Kayode na kunshe ne a wata sanarwa da fadar shugaban kasa ta fitar na sunayen sababbin shugabannin hukumomin tsaro na kasar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng