An Cafke Masu Kaiwa 'Yan Bindiga Makamai a Arewa, 'Yan Sanda Sun Yi Bayani

An Cafke Masu Kaiwa 'Yan Bindiga Makamai a Arewa, 'Yan Sanda Sun Yi Bayani

  • Jami’an sashen yaki da masu garkuwa da mutane na rundunar ‘yan sandan Kaduna sun cafke masu safarar makamai ga ‘yan bindiga
  • Wadanda ake zargin da suka amsa laifinsu, Abdulaziz Habibu da Nuhu Thomas mazauna Dogon Dawa ne da ke a Birnin Gwari
  • Rundunar 'yan sandan ta ce wadanda ake zargin suna safarar makamai ga wasu ’yan bindiga da suka addabi yankin Zariya da ke jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Rundunar ‘yan sandan Kaduna ta ce an kama wasu mutane biyu da ake zargi da yin safarar makamai ga 'yan bindiga a yankin Zariya da ke jihar.

A wata sanarwa da kakakin rundunar a Kaduna, Mansur Hassan ya fitar ya ce an kama wani wanda ake zargi yana kai kwarmato ga masu garkuwa da mutane da ke a dajin Gidan Dogo.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban majalisa ya kai agajin ambaliya a Yobe, ya tallafawa jama'a da miliyoyi

Rundunar 'yan sanda ta cafke masu safarar makamai ga 'yan bindiga a Kano
An cafke masu safarar makamai da kai rahoto ga 'yan bindiga a Kaduna. Hoto: @Princemoye1
Asali: Twitter

Kaduna: An cafke masu safarar makamai

DSP Hassan ya ce an kama mai kaiwa masu garkuwa bayanan wadanda za su sace, mai suna Abubakar Yahuza, a ranar 14 ga watan Agusta, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce mutanen biyu Abdulaziz Habibu da Nuhu Thomas mazauna Dogon Dawa ne a karamar hukumar Birnin Gwari ta Kaduna.

"Bayanan da suka bayar ya taimaka sosai a bincike da muke yi, kuma a halin yanzu suna ba 'yan sanda hadin kai da nufin ganowa tare da kamo wadanda ke da hannu a ciki."

- A cewar kakakin 'yan sandan.

An kubutar da wadanda aka sace

Channels TV ta rahoto wadanda ake zargin, sun shiga hannun jami’an ‘yan sanda masu yaki da garkuwa da mutane dauke da wata bindiga kirar AK-47 a kauyen Madaci da ke Zariya.

A cewar ASP Mansir Hassan, wadanda ake zargin sun amsa laifinsu da hannu wajen safarar makamai, inda suke kaiwa ’yan bindiga da suka addabi yankin Zariya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun matsawa mutane, sun farmaki kananan hukumomin Katsina

Jami’an ‘yan sanda sun kuma ceto wasu manoma biyu da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a kauyen Kuriga da ke karamar hukumar Chikun bayan musayar wuta a ranar 18 ga Agusta.

An cafke mata mai safarar makamai

A wani labarin, mun ruwaito cewa jami'an tsaro a jihar Katsina sun yi nasarar cafke wata mata mai suna Aisha Abubakar da ake zargi da yin safarar makamai ga 'yan ta'adda.

An gano tulin alburusai a cikin kayan da matar take dauke da su a lokacin da jami'an ke duba kayan da fasinjoji, inda nan take ta yi kokarin musanta cewa alburusan na ta ne.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.