Safarar makamai a Zamfara: Dubu 20 ake biya na AK-47, dubu 5 na harsasai

Safarar makamai a Zamfara: Dubu 20 ake biya na AK-47, dubu 5 na harsasai

  • Rahotanni sun bayyana yadda 'yan fashin daji ke safarar makamai tsakanin iyakokin Zamfara, Sokoto da Katsina
  • An gano cewa, ana bai wa mata da yara dubu ashirin na shigowa da AK-47, dubu 5 na harsasai a tsakanin kauyuka
  • Ana alakanta yawon miyagun makaman da harsasai da hadin bakin jami'an da ake baiwa cin hanci a iyakokin kasar nan

Zamfara - Murtala Rufa'i malami ne jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto, ya ce wani binciken da yayi kan ta'addanci a Zamfara ya bayyana yadda jama'a ke samun kudi daga safarar makamai.

A rahotonsa mai take, "Ni dan bindiga ne": Binciken shekaru 10 kan 'yan fashin daji a jihar Zamfara, Rufai ya ce binciken ya nuna cewa akwai sama da makamai 60,000 a arewa maso yamma, The Cable ta wallafa.

Kara karanta wannan

Jama’ar gari sun kashe wani da ake zargin dan fashi ne a Katsina

Safarar makamai a Zamfara: Dubu 20 ake biya na AK-47, dubu 5 na harsasai
Safarar makamai a Zamfara: Dubu 20 ake biya na AK-47, dubu 5 na harsasai. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ya ce kamar makamai kamar bindigogin harbi jirgin sama, abun harba gurneti, AK-47, AK-49, da sauransu duk ana samun su a sansanonin 'yan bindiga a jihar.

Kamar yadda Rufai ya ce, ya tattauna da 'yan bindiga kuma ya ziyarci wasu jihohi inda ya kara da cewa suna samun kudi ta cinikayyar makamai kuma suna kashe kudin ne wurin siyan kwayoyi, neman mata, caca, wayoyi da sauransu.

"Duk wani tushe na samar da makamai ya na yawo ne a bangaren barin iyakokin kasa a bude da kuma gazawar jami'an tsaro wurin toshe dukkan iyakokin kasar nan," rahoton ya ce, wanda aka gabatar a ranar 9 ga Satumba.
“A gaskiya akwai matsalar rashin jami'ai kuma da yawansu sun fi son a kai su iyakokin da ake samun kudi. Sau da yawa ana amfani da kananan iyakokin kasa wurin shigo da makamai."

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Jami'in dan sanda ya harbe abokin aikinsa dan sanda a jihar Kano

Ya ce akwai yuwuwar wasu daga cikin jami'an da ke iyakokin ke tayawa tare da taimakawa wurin shigo da makamai cikin kasar nan, The Cable ta ruwaito.

Da yawa daga cikin masu safarar makamai an gano cewa suna amfani da iyakokin Zamfara, Sokoto da na Katsina a yankin arewa maso gabas.

"Akwai mata da kananan yara da ake amfani da su wurin shigo da makamai. Da wuya ake samun mata masu safarar makamai, amma idan aka same su, sun fi kowa iya shigo da makaman.
“Dogaro da nisa da yanayin wurin, ana safarar AK47 a kan N20,000, yayin da harsasai da suka kai 100 ake safarar su kan N5,000
“Safarar harsasan ya fi sauki saboda basu da girma kuma ana iya raba su kashi-kashi, abinda mazauna yankunan ke kira da Geron Hajiya."

Marwa: NDLEA ta kwace miyagun kwayoyi na N6bn masu alaka da ISIS

A wani labari na daban, shugaban hukumar yaki da safarar miyagun kwayoyi ta NDLEA, Buba Marwa, ya bayyana yadda suka kwace miyagun kwayoyi masu kimar naira biliyan 6 a filin jirgin ruwa da ke Apapa, jihar Legas.

Kara karanta wannan

Da na sani ban yiwa yan bindiga afuwa a baya ba, Gwamna Aminu Masari

TheCable ta ruwaito cewa, ya yi wannan jawabin ne a ranar Laraba inda shugaban NDLEA din ya ce kwayoyin sun zo ne daga gabas ta tsakiya.

A cewarsa, hukumar ta samu bayanan sirri ne daga abokan huldar ta dangane da safarar kwayoyi ta filin jirgin Apapa. Marwa ya ce kwayoyin masu suna Captagon suna da alaka da kungiyar ‘yan ta’adda da ke gabas ta tsakiya, TheCable ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng