Airbus A330: Abin da Ya Kamata Ku Sani game da sabon Jirgin Shugaban Kasar Najeriya

Airbus A330: Abin da Ya Kamata Ku Sani game da sabon Jirgin Shugaban Kasar Najeriya

  • Gwamnatin tarayya ta yi magana kan dalilin sayawa shugaban kasa jirgin sama kirar Airbus A330 duk da ana fama da matsin tattali
  • Wani bincike da aka yi ya nuna cewa sabon jirgin shugaban kasar da aka saya ya shekara 15 da kerawa, kuma an sayo shi a kasar Sweden
  • An ce tun watan Mayu jirgin ya ke a ajiye a filin jiragen sama na Basle Mulhouse Freiburg kafin Najeriya ta sayo shi daga kamfanin AMAC

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya shilla zuwa kasar Faransa a ranar Litinin cikin sabon jirgin shugaban kasa da gwamnatinsa ta saya.

Kara karanta wannan

Jam'iyyun adawa sun hada kai, sun ragargaji Tinubu kan sayen sabon jirgi

Bincike ya nuna cewa jirgin ya sauka Najeriya ne a ranar Lahadi, 18 ga watan Agustan 2024, domin Tinubu ya yi tafiyar da shi.

Abubuwan da ya kamata ku sani game da sabon jirgin shugaban kasa
Gwamnati ta fadi dalilin sayen sabon jirgin shugaban kasa. Hoto: @NGRPresident
Asali: Twitter

An sayawa shugaban kasa sabon jirgi

Bayo Onanuga, daya daga cikin manyan masu magana da yawun Tinubu, a shafinsa na X ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Sabon jirgin sama kirar Airbus A330 zai maye gurbin Boeing B737-700 (BBJ) wanda aka saya tun zamanin shugaban kasa Olusegun Obasanjo."

Sai dai an samu ka-ce-na-ce game da sayen sabon jirgin, musamman ganin cewa tattalin arzikin Najeriya bai kai ga daidaituwa ba, ga kuma yunwa a kasa.

Abin da muka sani game da sabon jirgin

Binciken da kafar labaran BBC ta yi ya nuna cewa sabon jirgin da fadar shugaban kasar ta sayo, Airbus A330 ya shekara 15 da kerawa.

An ce a shekarar 2009 ne aka fara kaddamar da jirgin a wani kamfanin Saudiya mai suna Midroc Aviation, daga nan aka sayarwa kamfanin AMAC da ke Sweden a 2021.

Kara karanta wannan

Daga karin kumallo, uwa da ƴaƴanta 3 sun rasu a wani yanayi mai ban tausayi

An ce tun watan Mayu jirgin ya ke a ajiye a filin jiragen sama na Basle Mulhouse Freiburg kafin Najeriya ta sayo shi daga kamfain AMAC aka kawo shi kasar 18 ga watan Agusta.

Shafin mujallar Bloomberg ya nuna cewa an fara tallata jirgin ne a wani shafi na Aircarft21, wani dandali na saye da sayar da jiragen sama, a inda Najeriya ta gan shi.

Dalilin sayawa shugaban kasa sabon jirgi

Mai magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa sabon jirgin zai ceto Najeriya daga kashe makudan kudi kan mai da kula da shi.

Onanuga ya ce:

“Sabon jirgin da aka sayo a kasa da farashin kasuwa, ya ceci Najeriya daga kashe miliyoyin daloli a duk shekara na kudin mai da kula da shi."

Sayo sabon jirgi: Gwamnati ta take doka?

A wani labarin, mun ruwaito cewa wani bincike ya nuna fadar shugaban kasa ta yi biris da majalisa wajen sayowa shugaba kasa sabon jirgin sama.

Kara karanta wannan

An gano yadda fadar Shugaban kasa ta take doka da majalisa wajen sayen jirgin sama

An kuma bayyana cewa gwamnatin Najeriya ta fara cinikin jirgin a kan farashin $100m, amma ba a tabbatar da ainihin farashin da aka sallama shi ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.