Gwamna Ya Tono Illar Tallafin Lafiya, Ya Gindayawa Kungiyoyi Sharadin Taimako

Gwamna Ya Tono Illar Tallafin Lafiya, Ya Gindayawa Kungiyoyi Sharadin Taimako

  • Gwamnatin jihar Ribas ta ce ba za ta yadda ana jefa rayuwar mutanen jihar a cikin mawuyacin hali ba da sunan bayar da tallafi
  • Siminalayi Fubara ta ja kunnen kungiyoyin addini da sauran kungiyoyi kan bayar da tallafin kiwon lafiya ga mazauna Ribas
  • Kwamishinar lafiya ta ce daga yanzu ba a amince wata kungiya ta duba lafiyar kowane mazaunin jihar ba sai da sharadi

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Rivers - Gwamnatin jihar Ribas ta gargadi kungiyoyin addini da sauran kungiyoyi masu zaman kansu da su daina lafiyar mazauna yankin babu amincewar gwamnati.

A kan samu kungiyoyi masu zaman kansu na taimakawa jama'a, musamman mazauna karkara da duba lafiyarsu kyauta a bangarori daban daban.

Kara karanta wannan

NLC ta ja daga, ta fadi tsattsauran mataki idan aka kama shugabanta, Ajaero

Fubara
Gwamnatin Ribas ta ce sai da amincewarta kungiyoyi za su duba lafiyar jama'a Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa gwamnatin jihar ta ce dole ne sai duk wata kungiya da za ta taimaki jama'a ta hanyar duba lafiyarsu kyauta ta samu sahalewarta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishinar lafiya ta jiha, Dr. Adaeze Oreh ta ce an dauki matakin ne saboda kare al'ummar Ribas daga yiwuwar fadawa hannun jami'an lafiya na bogi.

Lafiya: Gwamnati ta sa wa kungiyoyi sharadi

Gwamnatin Ribas ta sanyawa kamfanoni, kungiyoyin addini da sauran kungiyoyi masu zaman kansu sharadin duba marasa lafiya kyauta domin kare lafiyar jama'a.

Kwamishinar lafiya, Dr. Adaeze da ta bayyana haka, ta kuma ce gwamnati ta garkame wasu asibitoci bisa aiki ba tare da cika sharuddan gwamnati ba.

Jaridar Independent News ta ce kwamishinar ta bayyana takaicin yadda wasu kungiyoyi da kamfanoni su ka ki tuntubar ma'aikatar lafiya gabanin duba marasa lafiya.

Gwamnati ta kawo dokar lafiya

Kara karanta wannan

Ambaliya: Gwamnatin Kaduna ta bullo da matakin ceton mazauna kananan hukumomi 7

A baya kun ji cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta samar da doka a fannin lafiya, wacce za ta rika jan linzamin likitocin da ke barin kasar nan sakaka.

Ministan lafiya, Farfesa Muhammad Ali Fate da ya bayyana matakin, ya ce an samar da dokar domin inganta lafiyar yan kasar nan da wadata asibitoci da jami'an lafiya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.