Ba Sani ba Sabo: Gwamnatin Abba Ta Dura kan Dan Uwan Kwankwaso domin Bincike
- Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Kano ta kafa kwamitin binciken dan uwan Rabi'u Kwankwaso, Musa Garba Kwankwaso
- Haka zalika binciken hukumar yaki da rashawan zai shafi shugaban ma'aikata, Alhaji Shehu Wada Sagagi
- Hukumar za ta binciki mutanen ne kan zargin karkatar da tallafin abinci da gwamnatin tarayya ta turo Kano da harkar magani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta fara gudanar da bincike kan tallafin abinci da shugaba Bola Tinubu ya turo da badakalar magani a jihar.
Hukumar na zargin ɗan uwan Rabi'u Kwankwaso ne mai suna Musa Garba Kwankwaso da shugaban ma'aikatan gidan gwamnati, Shehu Wada Sagagi.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban hukumar yaki da rashawa ta Kano, Muhyi Magaji ya ce za a yi bincike ba sani ba sabo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Za a binciki dan uwan Kwankwaso
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Kano za ta fara binciken Garba Musa Kwankwaso kan zargin badakalar magani bayan bidiyon Dan Bello.
Ana zargin cewa an ware makudan kudi domin kwangilar magani a dukkan ƙananan hukumomin Kano ga kamfanin Garba Musa, mai suna Novomed.
Za a yi bincike ne kan cewa ana zargin kwangilar da aka ba kamfanin ba ta cika ka'ida ba kuma kowace karamar hukuma za ta rika sayen maganin N9m daga Novomed duk wata.
Za a binciki shugaban ma'aikatan Kano
Haka zalika hukumar yaki da rashawa a Kano ta ce za ta binciki shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin Kano, Shehu Wada Sagagi.
Ana zargin Shehu Wada Sagagi ne da karkatar da abincin tallafi da gwamnatin tarayya ta tura jihar Kano zuwa wasu wurare na daban.
Hukumar yaki da rashawa ta ce duk da maganar tana gaban kotu, hakan ba zai hana ta tsoma baki a kan lamarin ba.
Bidiyon Dan Bello: Abba ya yi magana
A wani rahoton, kun ji cewa gwamna Abba Yusuf na jihar Kano ya musanta masaniyar ba kamfanin Novomed kwangilar sayowa kananan hukumomi 44 magunguna.
Fitaccen tsohon dan jaridar nan, Dan Bello ne ya fitar da wani bidiyo da ya ke ikirarin gwamnatin Kano ta saba ka'idar ba da kwangilar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng