Damina Mai Albarka: An Fara Ganin Saukin Abinci a Kano, jihohin Arewa Maso Yamma
Bayan shafe lokaci mai tsawo ana kuka a kan hauhawar farashin abinci a kasar nan, sauki ya fara samuwa a wasu daga cikin jihohin Arewa maso Yamma.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Farashin abinci ya fara yin kasa a wasu daga cikin kasuwannin da ke yankin Arewa maso Yamma bisa dalilai da yawa.
Jihohin da aka fara samun farashin abinci da sauki saukiakwai;
1. Kano: Farashi ya fara sauka
Jaridar Vanguard ta gano cewa sabon girbi ya fara karasawa kasuwanni, hakan ya jawo raguwar farashin wasu kayan abincin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gero da ake sayarwa a kan N90,000 yanzu ya koma N80,000, Masara da ake sayarwa N105,000 yanzu ta koma N95,000, shi ma wake ya dawo N130,000 daga N170,000.
Kayan miya ma ya na saukowa, inda yanzu ake sayar da kwandon tumatiri a kan N2,000 maimakon N3,200, ita kuma albasa ana sayarwa a kan N7000.
2. Ana samun saukin abinci a Kaduna
Manoman Kafanchan na jihar Kaduna sun ce damuna ta yi kyau, domin an samu yabanya, The Guardian ta wallafa wannan.
Amos Barnabas, wani babban manomi a yankin ya ce sun fara kai sabon amfanin gona kasuwanni, sai dai wasu jama'ar gari sun ce ba sa ganin saukin a kasuwa.
A kasuwar Anchau da ke ci duk mako a karamar hukumar Kubau da ke jihar, an samu saukin farashin masara, shinkafa, dawa da waken soya.
3. Katsina sun samu saukin farashin kayan gwari
Yayin da farashin hatsi ke sauka a makotansu, a jihar Katsina farashin kayan miya ne kawai ke saukowa, amma sauran su na nan da tsadarsu.
Albasa ta ki saukowa, domin manomanta sun ce ruwan bana ya illatata sosai.
Wasu mazauna jihar sun roki yan kasuwa da su daina boye kayan abinci domin tunanin samun kazamar riba.
Farashin abinci ya fara sauka a Arewa
A baya kun samu labarin yadda mazauna wasu jihohi a Arewacin kasar nan su ka fara murna bayan an fara samun raguwar farashin abinci a wasu kasuwanni.
An fara samun sassaucin tsadar kayan abincin ne a jihohi Kano, Taraba, Kwara da Neja jim kadan bayan zanga-zangar adawa da manufofin gwamnatin Tinubu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng