Abinci: Bayan Addu'o'in Talakawa, Farashi Ya Karye a Wasu Kasuwannin Arewa
- An fara samun sauƙin tsadar kayayyaki yayin da al'umma suka shiga damuwa kan hauhawar farashin kayan masarufi
- Rahotanni na nuni da cewa an samu sauƙin kayan gwari a kasuwannin yankin jihohin Arewa maso gabashin Najeriya
- Legit ta tattauna da yar jihar Yobe mai harkar dafa abinci domin jin ko saukar farashin ya fara tasiri kan masu sayen kayan gwari
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Arewa - Rahotanni da ke fitowa daga jihohin Arewa maso gabas na nuni da cewa an fara samun sauƙin kayayyaki.
'Yan kasuwa sun bayyana dalilan da suka sa aka samu sauƙin farashin kayan gwari a kasuwannin yankunan.
Jaridar Punch ta wallafa cewa sauƙin farashin ya shafi jihohin Yobe, Borno da Adamawa da ke Arewa maso gabas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Saukar farashin kayan gwari a Yobe
An ruwaito cewa farashin kayan gwari ya sauka da kashi 50% a Damaturu da ke jihar Yobe idan an kwatanta da kwanakin baya.
Kwandon tumatur da ake sayarwa N120,000 a watannin Mayu da Maris ya dawo N40,000 a yanzu haka.
Rahoton NAN ya nuna cewa an samu saukin farashin barkwano a jihar Yobe sai dai har yanzu farashin albasa bai sauko ba.
Sauƙin farashin kayan gwari a Borno
Kamar yadda yake a jihar Yobe, an samu saukar farashin kayan gwari a Maiduguri da ke jihar Borno.
Yan kasuwar kayan gwari a Borno sun ce suna cigaba da tsammanin karyewar farashin kayan cikin kwanaki masu zuwa.
Saukar farashin kayan gwari a Adamawa
Haka zalika a jihar Adamawa an samu sukar farashin kayan gwari sosai sai dai duk da haka farashin tsabar abinci kamar wake da gero ba su sauko ba.
Yan kasuwa sun bayyana fara cire amfanin gona da manoma suke a matsayin dalilin samun sauƙin farashin.
Legit ta tattauna da Asma'u Jibril
Wata mai harkar dafa abinci a Yobe, Asma'u Jibril ta bayyanawa Legit cewa su kam ba su ga alamun saukar farashin kayan gwari ba.
Asma'u ta ce su kam ma ganin kaya suka yi ya kara tsada idan suka sayo daga kasuwa, sai dai ba a san ko aga canjin a gaba ba.
An samu saukin abinci a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa farashin wasu kayayyaki kamar shinkafa, sukari, fulawa, taliyar indomi da dai sauran su ya fara sauka a kasuwannin Najeriya.
Wannan kuwa ya faru ne sakamakon darajar da Naira ta yi a kan Dalar Amurka da ma sauran kudaden kasashen waje kamar yadda rahotanni suka tabbatar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng