An Gano Yadda Fadar Shugaban Kasa Ta Take Doka da Majalisa Wajen Sayen Jirgin Sama

An Gano Yadda Fadar Shugaban Kasa Ta Take Doka da Majalisa Wajen Sayen Jirgin Sama

  • An shiga zargin cewa fadar shugaban kasa ta yi watsi da dokokin kasar nan wajen sayowa shugaban kasa sabon jirgin sama
  • Wani bincike ya bankado cewa gwamnatin tarayya ba ta nemi sahalewar majalisun kasar nan ba kafin sayo jirgi daga wani banki a Jamus
  • A cikin shekarar nan ne aka samu bullar labarin cewa fadar shugaban kasa ta sayo wa shugaba Bola Tinubu gwanjon jirgin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Wani bincike ya gano cewa fadar shugaban kasa ta yi biris da majalisar dokokin kasar nan wajen sayowa shugaba Bola Ahmed jirgi.

Kara karanta wannan

Bayan caccakar Tinubu: Obasanjo ya fadi abin da ke kawo cikas ga ci gaban Najeriya

A watan Yuni ne aka sansu bullar labarin cewa gwamnatin kasar nan ta sayo sabon jirgin sama Airbus A330 daga wani banki da ke kasar Jamus.

Tinubu
Bincike ya gano cewa gwamnati ba ta bi ta majalisa ba kafin sayawa shugaba Bola Tinubu sabon jirgi ba Hoton: Ajuri Ngelale
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa tun daga fara shirin sayen jirgin, jami'an gwamnatin tarayya su ka yi gum da bakunansu a kan lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kuma tun bayan lokacin ba a samu wani bayani ko takarda a gwamnatance kan karin sabon jirgin da Najeriya ta yi ga jiragen shugaban kasa ba.

Babu wanda ya san farashin jirgin Tinubu

Premium Times ce ta wallafa cewa an tabbatar fadar shugaban kasa na kokarin sayen kasaitaccen jirgin da wani bankin Jamus ya kwace daga hannun wani Yariman Saudiyya.

An bayyana cewa gwamnatin kasar nan ta fara cinikin jirgin a kan farashin $100m, amma ba a tabbatar da ainihin farashin da aka sallama shi ba.

Kara karanta wannan

Miyagu sun nuna karfin hali, sun kashe jami'in gwamnati kusa da gida a Nasarawa

A wancan lokaci, shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya ce idan har bukatar da zo gabansu, za su gaggauta amincewa da bukatar shugaban.

An sanya jiragen shugaba Tinubu a kasuwa

A wani labarin, mun ruwaito cewa fadar shugaban kasa ta kaɗawa wasu tsofaffin jiragen Bola Ahmed Tinubu guda uku kararrawa a kasuwa bisa umarnin shugaban kasa.

Tinubu ya dauki matakin domin rage kashe kudi, kuma haka zai rage yawan jiragen da shugaban kasa ke da su daga jirage shida da masu saukar angulu guda hudu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.