'Yan Bindiga Sun Kashe Hadimin Gwamna da Matarsa, 'Yan Sanda Sun Magantu
- Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da kashe wani Sanusi Gyaza, mataimaki ga gwamnan jihar, Malam Dikko Radda
- An ruwaito cewa 'yan bindigar sun shiga har cikin gidan Sanusi Gyaza da ke karamar hukumar Kankia inda suka kashe shi
- Bayan kashe hadin gwamnan, an ce 'yan bindigar sun kashe uwar gidansa tare da yin garkuwa da amaryarsa a ranar Juma'a
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Katsina - Wasu ‘yan bindiga sun kai hari gidan Sanusi Ango Gyaza, mai taimaka wa gwamnan Katsina, Malam Dikko Radda a Gyaza, da ke karamar hukumar Kankia.
Gyaza, wanda tsohon shugaban kungiyar malamai ta Najeriya NUT na karamar hukumar Kankia ne, an kashe shi a harin tare da matarsa kamar yadda rahoto ya nuna.
'Yan bindiga sun kashe hadimin gwamna
Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta bakin kakakinta Abubakar Sadiq, ta tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin, inji rahoton Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ruwaito Abubakar Sadiq yana mai cewa, “Eh, muna sane kuma muna kan bincike.”
Jardar Sahara Reporters ta ruwaito cewa 'yan bindigar sun kashe hadimin gwamna da uwar gidansa a gidansa da ke unguwar Gyaza da ke Kankia a ranar Juma’a.
Ayyukan 'yan bindiga na ta'azzara a Katsina
An kuma tattaro cewa a yayin harin, ‘yan bindigar sun sace matarsa ta biyu, lamarin da ya jefa al’umma cikin firgici da jimami.
Al'umma sun nuna damuwa game da yadda matsalar tsaro ke kara tabarbarewa a jihar, inda ayyukan ’yan ta'adda da suka hada da garkuwa da mutane da kashe-kashe ke karuwa.
Da aka tuntubi babban daraktan yada labarai na gwamnan jihar Maiwada Danmallam, bai amsa sakon da aka aikawa lambar wayarsa da aka sani ba har zuwa hada wannan rahoto.
'Yan bindiga sun kashe dan siyasa a Katsina
A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yan bindiga sun kai hari ƙauyen Mairuwa da ke ƙaramar hukumar Faskari a jihar Katsina inda suka kashe wani dan siyasa, Alhaji Lado.
Wata majiya da ta bayyana marigayin a matsayin ɗan kasuwa, ɗan siyasa kuma babban manomi, ta ce marigayin an kashe shi ne lokacin da ya ƙi yarda ya bi ƴan bindigan.
Asali: Legit.ng