Ana Tsaka da Cacar Baki kan Bidiyon Dan Bello, Abba Ya Runtumo babban Aiki a Kano
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince a fara gina titin Dorayi zuwa Panshekara yayin da kira-kirayen al'ummar Kano ya yawaita
- An ce an gagara karasa aikin gina titin wanda gwamnatin tarayya ke yi tun a zamanin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari
- Gwamnatin Kano ta jaddada kudirinta na samar da ingantattun kayayyakin more rayuwa da za su amfanar da al’umma baki daya
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Gwamnatin Kano ta kaddamar da fara aikin gina titin Dorayi zuwa Panshekara wanda mutanen yankin suka dade suna rokon a yi masu.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya daura damarar kammala wannan aikin hanyar wanda aka ce gwamnatin tarayya ta gaza kammalawa.
Mai kaiwa gwamna rahoto daga ma'aikatar ma'aikatun jihar, Khamis Bashir Bako Ayagi ne ya sanar da hakan a shafinsa na Facebook ranar Asabar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kano: An fara gina titin Dorayi-Pansheka
Khamis Ayagi ya ce an gagara karasa aikin gina titin wanda gwamnatin tarayya ke yi tun a zamanin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Sanarwar mai kaiwa gwamnan rahoto ta ce:
"Matakin fara wannan aikin titin ya zo ne a matsayin martani ga kiraye-kirayen da mazauna Kano suka dade suna yi kan rashin kammala aikin gwamnatin tarayyar.
Gwamnatin jihar, ta lura da bukatar inganta harkokin sufuri, inda ta dauki kwararan matakai domin magance wannan muhimmin gibin na samar da ababen more rayuwa."
Gwamnatin za ta gina ababen more rayuwa
Mai girma kwamishinan ayyuka da gidaje na Kano, Injiniya Marwan Ahmed Aminu ya kai ziyarar gani da ido domin tantance yadda aikin gina titin ke gudana.
Kwamishinan ya jaddada kudirin gwamnati na samar da ingantattun kayayyakin more rayuwa da za su amfanar da al’ummar Kano baki daya.
Da wannan gagarumin aiki, gwamnati ta nuna jajircewarta wajen inganta rayuwar al’ummarta ta hanyar inganta ababen more rayuwa, a cewar Khamis.
Mazauna Kano sun yi godiya ga Abba
A zantawarmu da Abba Hassan mazaunin Dorayi, ya ce wannan aikin titin ya dade yana ciwa kowanne mazaunin yankin tuwo a kwarya.
Abba Hassan ya ce yana fatan gwamnatin Abba Yusuf za ta kammala aikin, domin gaza kammala aikin barazana ce ga yankin saboda kasancewarta hanyar ruwa.
Anam Dorayi shi ma ya nuna godiyarsa ga hobbasar gwamantin Abba na daukar dawainiyar dawo da aikin gina titin, inda ya ce Allah ne ya amsa addu'arsu.
Kamar Abba, shi ma Anam ya yi kira ga Gwamna Abba da ya taimaka ya karasa titin domin gudun ka da abin da ya faru a gwamnatin baya ya maimaita kansa.
Bidiyon Dan Bello: Abba ya yi martani
A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamna Abba Yusuf ya yi martani ga wani bidiyo da Dan Bello ya wallafa wanda ya yi ikirarin gwamnatin Kano ta ba da kwangila ba bisa ka'ida ba.
Gwamna Abba ya ce ba shi da masaniyar an ba wani kamfani kwangilar samar da magunguna na kusan N8bn ga kananan hukumomin jihar, amma ya sa ayi bincike.
Asali: Legit.ng