An Zargi Gwamnatin Shugaba Tinubu da Satar Dabarar Tattalin Arziki a Wajen Atiku
- Ministan kudi da tattalin arziki ya nuna za a yafewa wasu kamfanoni haraji idan suka dauki ma’aikata da yawa
- Magoya bayan Atiku Abubakar sun fara cika-baki, su na cewa wajen ‘dan takaran na PDP aka sato wannan tsari
- Amma an gano cewa dama can Bola Tinubu yana da wannan ra’ayi, tunaninsu ya zo daidai na Alhaji Atiku ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja – Ministan kudi da tattalin arzikin Najeriya, Mista Wale Edun ya na ta kokarin ganin ya farfado da tattalin arzikin kasar nan.
A yunkurin ministan ne ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta na tunanin yafe karbar haraji daga hannun wasu kamfanoni.
Tinubu zai kawo tsarin afuwar haraji
Kamfanonin da za a yi wa afuwar harajin su ne wadanda su ka dauki karin ma’aikata, Nairametrics ta kawo wannan rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta na kuma duba yiwuwar yafe karbar harajin shigo da wasu kayayyaki domin magance tsada a kasar.
Ministan kudin ya amince cewa an shiga matsin lamba saboda Naira ta rage daraja a yau.
"Idan ka dauki Karin ma’aikata, za a yi maka afuwa da biyan haraji. Saboda haka dabaru ne da shugaban kasa zai sa hannu a kansu."
- Wale Edun
An ce Tinubu ya saci dabarun Atiku
Da jin wannan sanarwa sai ‘yan adawa suka fara murna, su na ikirarin gwamnatin Tinubu ta sato dabarar ne wajen Atiku Abubakar.
“Sun dauko wata dabarar daga Atiku, kuma kamar sauran, ba za su aiwatar da kyau ba, sai su fito suna cewa ‘ko Atiku haka zai yi’
Nan take wasu suka maidawa @chosensomto amsa a shafin Twitter, su ka ankarar da shi cewa ba satar wannan tsari aka yi.
Legit Hausa ta ci karo da wani bidiyo da Chibuzo Mikel ya wallafa a dandalin, a nan aka ji Bola Tinubu yana irin wannan magana.
Da gaske Tinubu ya ari dabarar Atiku?
A wajen wani taro lokacin yakin zaben 2023, Tinubu ya shaidawa duniya yana da wannan tunani a ran shi idan ya karbi mulki.
Shi Atiku ya fadi manufar yin hakan, ‘dan takaran na APC a lokacin ya ki fito da dabarar a fili saboda gudun a saci fikirarsa.
Malami ya shako kuren Bola Tinubu
Ana da labari a hudubar Dr. Bashir Aliyu Umar bayan zanga-zanga, ya ce tun farko gwamnati tayi kuskure a harkar tattalin arziki.
Zanga-zangar da aka yi ta zama hanyar ta’adi maimakon nuna adawa da manufofin Bola Tinubu, dama can an yi gargadin irin hakan.
Asali: Legit.ng