An Binciko Attajiri a Gwamnatin Tinubu Mai Shigo da Man Fetur daga Kasar Malta

An Binciko Attajiri a Gwamnatin Tinubu Mai Shigo da Man Fetur daga Kasar Malta

  • Abdulkabir Adisa Aliu ya na cikin ‘yan kasuwar da su ke shigo da fetur Najeriya daga kasar Malta a nahiyar Turai
  • Ana tunanin Matrix Energy mai gidajen mai 150 ya shigo da kusan 25% na duka fetur din da aka sha kwanan nan
  • Alhaji Abdulkabir Adisa Aliu ya na cikin kwamitin PCCC, wannan ya tabbatar da zancen da Aliko Dangote yake yi

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - A ‘yan kwanakin nan an yi ta magana a game da yadda ake shigo da mai daga kasar Malta bayan zancen Aliko Dangote.

Attajirin Afrikan ne ya fara fitowa ya na zargin cewa akwai manya a cikin gwamnatin tarayya da su ke gyara mai a Malta.

Kara karanta wannan

Sheikh Bashir Aliyu Umar: Kuskuren farko da Tinubu ya yi daga hawa mulkin Najeriya

Abdulkabir Adisa Aliu
Abdulkabir Adisa Aliu yana shigo da fetur daga kasar Malta Hoto: matrixenergygroup.com/@DOlusegun
Asali: UGC

Ana kawo man fetur daga kasar Malta

Duk da shugaban NNPCL, Mele Kolo Kyari ya musanya zargin, rahoton The Cable ya tabbatar da abin da ‘dan kasuwan ya fada.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gano cewa daya daga cikin wadanda su ke shigo da mai daga wannan karamar kasa da ke Turai yana cikin gwamnatin tarayya.

Kasuwancin Abdulkabir Adisa Aliu a Malta

Abdulkabir Adisa Aliu wanda shi ne shugaban kamfanin Matrix Energy yana cikin ‘yan kasuwan da ke shigo da mai daga Malta.

Da aka zanta da shi, Alhaji Abdulkabir Adisa Aliu ya nuna kasuwancin mai tsabta, yake yi, babu ha’inci a harkar neman kudin nasa.

Bayanan da aka samu sun nuna cewa a watan Yulin 2024 kadai, an shigo da tan sama da 200, 000 na mai daga Malta zuwa Warri.

Tinubu ya ba Abdulkabir Adisa Aliu mukami

Kara karanta wannan

Gwamna ya jingine Atiku, ya faɗi mutum 1 da ya kamata ya karɓi mulkin Najeriya a 2027

Kamar yadda The Guardian ta rahoto a watannin baya, Abdulkabir Adisa Aliu yana cikin ‘yan kwamitin shugaban kasa na PECC.

A farkon shekarar nan Bola Tinubu ya rantsar da wannan kwamiti domin taimaka masa da dabarun farfado da tattalin arziki.

Ana tace fetur a kasar Malta da kyau?

Ana zargin man da ake shigowa da shi daga Malta bai da kyau sosai, zargin da shugaban kamfanin na Matrix ba zai karba ba.

Kamfanonin da ke Malta ba su iya tace mai, sai dai su gyara danyen man da aka riga aka tace ta hanyar cire ruwa ko wata kazanta.

Tsoron da ake yi shi ne akwai sinadarin naphtha wanda yake lalata na’urori a Najeriya ba tare da mutane sun iya ganewa ba.

Yunkurin batawa matatar Dangote suna

Ana murna za samu tafkekiyar matatar mai a Afrika a dalilin Alhaji Aliko Dangote, sai aka ji labari ana neman ganin bayansa.

David Hundeyin ya ce ya ki karbar kusan N1, 000, 000 domin ya yi rubutun da zai soki matatar man Dangote da aka gina a Legas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng