Jerin Kamfanoni guda 50 da Najeriya ta baiwa kwangilar hakar danyen mai a shekarar 2018

Jerin Kamfanoni guda 50 da Najeriya ta baiwa kwangilar hakar danyen mai a shekarar 2018

Kimanin kamfanonin guda hamsin, 50, ne gwamnatin Najeriya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta baiwa kwangilar aikin hakar danyen mai na shekarar 2018/2019, inji rahoton jaridar Premium Times.

Kamfanonin sun fito ne bayan wata fafatawa da aka hukumar albarkatun man fetir ta kasa, NNPC ta shirya na gwajin karfin kamfani da kuma kwarewarsa a harkar hakar danyen mai a watan Janairun da ta gabata.

KU KARANTA: Gungun yan fashi da makami sun kai farmaki wani Banki, sun kashe mutane 2

Majiyar Legit.ng ta ruwaito duk da yake ba’a sanar da sunayen kamfanonin da suka samu nasara a hukumance ba, amma babban manajan sashin siyar da man fetir na hukukmar NNPC, Mele Kyari ya bayyana wasu daga cikin sharuddan da kamfanonin suka cika

Jerin Kamfanoni guda 50 da Najeriya ta baiwa kwangilar hakar danyen mai a shekarar 2018
Kamfanin NNPC

Daga cikin sharuddan akwai: karancin kudin da suka shigo ma kamfani a shekarar 2016 kada ya gaza dala miliyan 600, da kuma karfin arzikin kamfanin kada ya gaza dala miliyan 250 a shekarar 2016, sauran sun hada da kokarin siyar da man Najeriya a kasashen waje, da kuma samar da shaidar samun dala daga babban banki.

Ga jerin kamfanonin da sunayen shuwagabanninsu:

1 AA Rano ALH (Dr) AUWALU ABDULLAHI RANO

2 Aipec oil and gas limited Tayo Awogboro

3 AMG Mr. Risqua Murtala Muhammed (Group CEO)

4 Arkleen Bruce Wilson

5 Augusta Giuseppe Nestola

6 Barbedos Mr. Shafii Aliyu

7 BB Energy Khaled Bassatne

8 Bono Energy Banjo Omisore

9 Calson NNPC

10 Cassiva Alhaji Nasiru H. Danu

11 Cepsa Mr. Pedro Miro Roig

12 Cretus

13 Emadeb Mr. Adebowale Olujimi

14 Eterna Mr. Mahmud Tukur

15 Gladius Commodities Omotayo Dina

16 Glencore Ivan Glansenberg

17 Hinstock

18 HPCL Mr. Mukesh Kumar Surana

19 Leighton Bowale Jolaoso

20 Levene Temitayo Ogunbanjo

21 Litasco Tim Bullock

22 Masters Energy Uchechukwu Samson Ogah

23 Matrix Abdulkabir Adisa Aliu

24 Mocoh Micheal Hacking

25 MRS Mr. Andrew Gbodume

26 North West Mrs. Winifred Akpani

27 Oando Adewale Tinubu

28 Ocean bed (Sahara) Tonye Cole

29 Petraco Ingeborg Srenger

30 Petrogas Usama Al Barwani

31 Propetrol Harry Ebohon

32 Prudent Abdulwasiu Sowami

33 Sacoil ( Efora Energy) Dr Thabo Kgogo

34 Sahara Tonye Cole

35 SEER

36 Setana Energy Edward Edozien

37 Setraco Chief Abu Inu- Umoru

38 Shoreline Kola Karim

39 Socar Arzy Azimov

40 Sonara Ibrahim Talba Malla

41 Total Mr Alexis Vovk

42 Trafigura Jeremy Weir

43 Ultimate gas (Rahamaniyya) Rahamaniyya

44 Vitol Russell Hardy

45 Voyage Hajiya Bola Shagaya

46 West African Gas Walter Perez

47 Zitts and Lords Okojie Samuel

48 ZR Energy ( Trafigura)

49 Obat oil and gas Prince Femi Akinruntan

50 Duke oil Mr Inuwa Waya

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng