Sheikh Bashir Aliyu Umar: Kuskuren Farko da Tinubu Ya yi Daga Hawa Mulkin Najeriya

Sheikh Bashir Aliyu Umar: Kuskuren Farko da Tinubu Ya yi Daga Hawa Mulkin Najeriya

  • Dr. Bashir Aliyu Umar ya ce kuskuren da bankin CBN ya yi ya taimaka wajen tabarbarewar tattalin arzikin kasa
  • Malamin ya koka kan yadda Yemi Cordoso ya shafe wata da watanni babu mataimaka a babban bankin CBN
  • Sheikh Bashir ya yi tsokaci kan yadda Naira ta karye bayan gwamnatin Bola Tinubu ta tabbatar da cire tallafin fetur

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Dr. Bashir Aliyu Umar malamin addini ne kuma masanin tattalin arzikin zamani musamman a bangaren tsarin musulunci.

Shehin malamin ya yi huduba kwanakin baya, inda aka ji ya yi kira ga talakawa da masu mulkin da suke rike da madafan iko a kasar.

Bola Tinubu
Bola Tinubu da Muhammadu Buhari wajen taron magabata a Abuja Hoto: @PBATMediaCentre
Asali: Twitter

Huduba ta tabo tsare-tsaren Bola Tinubu

A wannan huduba wanda Legit Hausa ta saurara a shafin malamin a Facebook, ya yi magana ne game da neman tsari daga fitintinu.

Kara karanta wannan

Matatar mai: Dan jaridan da aka yi wa tayin N800, 000 ya fallasa masu son karya Dangote

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dr. Bashir Aliyu Umar ya ja kunnen al’umma ganin yadda zanga-zangar lumanar da aka shirya ta rikide ya zama barna da tashin-tashina.

Limamin na masallacin Al-Furqan ya waiwayi gwamnatin Bola Tinubu, yake cewa ta yi wasu kura-kurai ta fuskar tsarin tattalin arziki.

Malamin yana ganin cewa an yi kuskure waje janye tallafin fetur har ana zargin an dawo da shi saboda an bar Naira tana gantali a kasuwa.

Inda bankin CBN ya yi kuskure

Yake cewa an sauke gwamnan babban banki aka daura na rikon kwarya sannan aka shiga binciken mataimakan gwamnoni a lokacin.

Abubuwan da suka faru a farkon mulkin Bola Tinubu da tsarin da aka kawo ya yi sanadiyyar da Dala ta rika sukuwa a kan Naira.

Baya ga cewa Yemi Cordoso bai da mataimaka, Sheikh Bashir ya ce gwamnan na CBN bai da ido a harkar aikin babban bankin kasa.

Kara karanta wannan

Tallafin Tinubu: Abba Kabir ya fusata da zargin APC, ya fadi yadda aka yi game da zargin badakala

Tinubu: Bashir Aliyu ya yi kira da yabo

Kafin ya bar mimbari sai da yabi wasu tsare-tsaren kamar saidawa Dangote mai a Naira, ya ce wannan zai sa a rage bukatar Daloli.

Har ila yau, ya yi kira ga gwamnonin jihohi su horar da matasa ta yadda za su samu sana’o’i, hakan zai rage zaman kasha wando.

Hudubar limamin ta kawo misali da wasu daga cikin tsare-tsaren da gwamnatin Muhammadu Buhari ta kawo kamar N-Power.

Malamin ya yabawa irinsu jihar Bauchi wanda ta iya rajistar wadanda suka amfana da tsarin, saboda haka matasa suka ci moriya da kyau.

Ana so Tinubu ya cire riba a NYIF

A wani rahoto na musamman, kun ji matasa suna son tallafin jari, amma gwamnati ta cusa ruwa a ciki wanda ya sabawa musulunci.

An yi kira ga gwamnatin Bola Tinubu da 'yan majalisar tarayya su fito da hanyoyin da musulmai za su ci moriyar tsare-tsare mara ruwa.

Kara karanta wannan

Abubuwan da suka wakana a taron Tinubu da tsofaffin shugabannin Najeriya a Aso Rock

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng